Back to Africa Check

Lemon Zoɓo baya maganin zazzaɓi- aje asibiti

Wani rubutu da aka buga a Facebook yayi iƙirarin cewa lemon zoɓo “na maganin zazzaɓi.”

“ Yadda ake lemon zoɓo na magani,” rubutun ya fara. Ya bayyana yadda za ayi  lemon da a fara  jiƙa ganyen zoɓo, abarba, ganyen lemongiras, citta, biturut, lemon zaƙi, kankana da ruwa.

Zoɓo dai wani lemo ne da ya shahara a Najeriya, wanda ake yi da busasshiyar filawar itacen rosilli. Itacen rosilli, wanda ake kira da habiscus sabdariffa a kimiyance ya fito ne daga ayarin itatuwan Malvaceae. Yana fitowa a wurare masu zafi, yana kuma da launin kore mai duhu ko jajayen kara da ganye.

Shin lemon da aka bayyana a rubutun yana maganin zazzaɓi? 

Zobofever_incorrect

 

Abubuwa da dama na jawo zazzaɓi

Zazzaɓi shine ƙaruwar zafin jiki sama da maki 37 a ma’aunin selshiyos. Wanda ke nuna alamun shigar cuta, kamar yadda Mayo Clinic suka bayyana. 

Wasu daga cikin alamun zazzaɓi sun haɗa da ciwon kai, rawar jiki, rashin ɗanɗano, rashin ruwa a jiki da kuma kasala. 

Hukumar lafiya ta Britaniyya(NHS) tace abubuwa da cututtaka da dama na iya jawo zazzaɓi. Yana kuma daga cikin alamun cutar Covid-19.

Mutane- manya da yara- idan zazzaɓi ya kama su tare da ciwon kai mai zafi, jijjiga, rikicewar tunani, yawan amai, ciwon ciki da wahala wajen numfashi, ana basu shawarar zuwa asibiti cikin gaggawa.

Kada a ɗauki zazzaɓi akan abu mai sauƙi

“Wannan haɗin gargajiya ne, ayi watsi da shi,” Cewar Marycelin Baba, Farfesa a fannin ƙwayoyin cuta ta jami’ar Maiduguri, kamar yadda ta shaidawa Africa Check.

Baba wadda suka wallafa wata takarda akan gaza gane cutar zazzaɓin cizon sauro da zazzaɓin taifot. “ Babu wata hujja a kimiyance da ta goyi da bayan wannan da’awar,”  cewar Farfesar. “Wannan haɗi baya magani ko hana zazzaɓi. Ƴaƴan itatuwan da aka lissafa na da muhimmanci a jiki amma ba maganin zazzaɓi ba ne”.

Baba ta ƙara da cewa: "Idan an kamu da zazzaɓi, a hanzarta zuwa asibiti. Kada a dogara da haɗe-haɗe. Kada a ɗauki zazzaɓi da wasa”

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.