“Ɗaukar malaman makaranta da dama a ma’aikatar ilimi ta tarayya” kanun wani saƙo da ke yawo a WhatsApp da Facebook a Najeriya a watan Nuwamba 2021.
“A ƙoƙarin ganin cewa an bunƙasa aikin koyarwa don kyautata ilimi, ma’aikatar shugaban ma’aikata ta ƙasa tana gayyatar waɗanda suke da sha’awar komawa aikin koyarawa daga ma’aikatan gwamnatin tarayya, da su tura takardar neman aikin,” saƙon ya ce.
Saƙon ya jero jerin darusa, waɗanda saƙon yace ana buƙatar masu sha’awar gurbin aikin ya kasance suna da digiri na farko a kai, sannan aka bada link na wani shafin yanar gizo.
Shin waɗannan guraben aiki gaskiya ne? Mun bincika.
Babu wani gurbin neman aiki
Lokacin da Africa Check ta ziyarci shafin yanar gizon da aka bada link a rubutun, mun ci karo da wata takarda wadda tayi kama da ta fito daga ofishin shugaban ma’aikata na ƙasa wadda kwanan watan da ke jikin ta ya nuna ranar 23 ga watan Juli 2021. Amma kuma link ɗin da shafin ke cewa a latsa don tura takardar neman aiki zai saƙe dawo da mutum shafin da ya ke kai ne.
Sai kuma muka bincika shafukan ma’aikatar ilimi ta ƙasa, ma’akatar ɗaukar ma’aikata da shafin ofishin shugaban ma’aikata na ƙasa, amma bamu samu inda aka yi maganar ɗaukar malaman makarantar ba.
Haka nan babu wata babbar kafar yaɗa labarai a Najeriya da ta kawo rahoton hakan.
Saka neman aikin da babu shi a Facebook abu ne da zai iya karkata tunanin mutane. Kuyi watsi da irin waɗannan saƙonnin da ke cewa ma’aikatar ilimi ta ƙasa na ɗaukar ma’aikata a watan Nuwambar 2021.
Don sanin hanyoyin kaucewa ƴan damfara a yanar gizo, ku karanta wannan.
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment