Back to Africa Check

Majalisar jihar Legas bata fitar da dokar kafa Shari’a don ta taimaki ɗan takarar shugaban ƙasa ba

Wani hoton allon waya wato  sikirinshut na wani shafin yanar gizo da ba’a san shi ba, wanda aka rarraba a Facebook da WhatsApp a Najeriya a tsakiyar watan Julin 2022, yayi iƙirarin cewa jihar Legas ta fitar da dokar ƙirƙirar kotunan shari’ah a jihar. 

Shari’a itace dokar shari’ar addinin islama, wadda musulmi ke ɗaukar ta a matsayin dokar ubangiji, wadda ke samar da ayyukan da masu imani zasuyi. 

“Majalisar jihar Legas a sihirce ta fitar da dokar Shari’a a wani shiri na ganin cewa sun samu goyan bayan ƴan arewa ga Tinubu,” rubutun da ke jikin hoton allon wayar ke cewa

Rubutun ya cigaba da cewa: “Ƙosawar Bola Tinubu ta kai ƙololowa, bayan mun yi zaton ba zai durƙusawa iyayen gidansa ƴan arewa ba.” 

Tinubu ne ɗan takarar shugaban ƙasar Najeriya a zaɓe mai zuwa daga jami’iyya mai mulki wato All Progressive Congress, zaɓen da aka shirya yi a watan Fabrairun 2023. 

Rubutun da ke jikin hoton allon wayar na cigaba da iƙirarin cewa majalisar jiha “a ɓoye kuma a cikin hanzari ta fitar da dokar ƙirƙirar kotun shari’a a Legas, wadda tuni gwamna mai ci a yanzu ya amince ta zama doka”. 

An buga makamanciyar wannan da’awar a wani wuri daban a Facebook. 

Wannan labarin sahihi ne? Mun bincika. 

Sharia_False

An bayyana da’awar a matsayin ‘ƙarya’

Majalisar jihar Legas ta ce a shafinta na Twita a ranar 13 ga watan Yuli labarin ƙarya ne. 

Cikakkiyar sanarwar da Setonji David, shugaban kwamitin watsa labarai, tsaro da tsare-tsare na majalisar ya fitar, na cewa: “An jawo hankalin majalisar jihar Legas akan wani rahoto da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, cewa majalisar a ɓoye ta kafa dokar shari’ah a wani shiri na neman samun goyan bayan ƴan arewa ga Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a jami’iyyar APC. 

“Ba mu so mu darajanta wanda yayi wannan rubutu ba, amma ya kamata mu fayyace gaskiya, wannan kawai al’mara ce daga marubucin, kuma ƙarya ce gaba ɗayanta.”

David ya ƙara da cewa hanyar da ake bi don kafa doka a bayyane take ga dukkan al’umma: “Ba za’a iya miƙa doka a jihar Legas ba tare da an zauna an saurare ta ba a bainar jama’a.”

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.