A taƙaice: Babu hujjar da ta tabbatar cewa Ifeanyi Okowo ya kira masu biyayya ga ɗan takara daga jam’iyyar Labour Peter Obi “taron mayunwatan rayuka marasa aikin yi”. Waɗannan kalamai da suka karaɗe yanar gizo na cikin labaran ƙarya da ke ta yawo gabanin zaɓen ƙasa na 2023.
“Masu biyayya taron mayunwatar rayuka ne marasa aikin yi,” cewar wasu kalamai da aka danganta ga ɗan siyasar Najeriya Ifeanyi Okowo. Saƙon nata yaɗuwa a Facebook tun 11 ga watan Oktoba 2022.
Masu biyayya magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa ne daga jam’iyyar Labour Peter Obi. Ƴan Najeriya masu zaɓe zasu zaɓi sabon shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu 2023.
Okowa kuma gwamnan jihar Delta ne da ke Kudancin Najeriya. Shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa ga Atiku Abubakar daga jami’iyyar adawa ta People’s Democratic Party.
Za’a iya ganin kalaman a Facebook a nan, nan da nan.
Shin Okowa ya faɗi hakan? Mun bincika.

Labaran ƙarya na cutar zaɓin’ masu zaɓe
Babu ɗaya daga cikin rubutun na Facebook da ya bayyana cikakken waje da lokacin da Okowa yayi wannan furuci. Wannan rashin hujja babbar alama ce da ke nuna labaran ƙarya.
Haka nan ba’a samu kalaman a sahihin shafin Okowa na Tiwita ba. Haka nan ba’a samu rahoton hakan daga manya gidan jaridar ƙasar ba.
An fara yaƙin neman zaɓen ƙasar na 2023 a ranar 28 ga watan Nuwamba.
Tun bayan nan- da kafin nan- ana ta samun yawaitar da’awar ƙarya akan ƴan takara da jam’iyyu. Waɗannan zasu iya gurɓata muhawarar siyasa, su kuma ragewa masu kaɗa kuri’a damar zaɓen wanda suke da cikakken sani a kai.
Don samun ƙarin bayani, ku duba hanyoyin sanin babban zaɓen Najeriya mai muhimmanci na 2023.
Republish our content for free
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment