Back to Africa Check

Ministan yaɗa labaran Najeriya Mohammed bai ce ɗan takarar shugaban ƙasa Obi na da hannu a cikin rikicin #EndSARS ba

Ministan yaɗa labaran Najeriya Lai Mohammed ya tuhumi ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar Labour Peter Obi da cewa shi ne “wanda ya haddasa” rikicin #EndSARS, cewar wasu saƙonni da ke yawo a  Facebook tun watan Yuli 2022

“Wasu abubuwan da suka faru a kwana-kwanan nan sun bayyana wanda ya haddasa rikicin ENDSARS a Najeriya, wanda ya jawo asarar kadarorin gwamnati da mutuwar jami’an tsaro,” ɗaya daga cikin mafi tsaho daga saƙonnin ke cewa

#EndSARS da akayi akan nuna ƙin amincewa da gallazawar da ƴan sanda masu ƴaki da ƴan fashi ke yiwa jama’a, an fara ta ne a Tiwita inda ta zarce har zuwa titunan  Najeriya. A watan Oktoba 2020, ƴan sanda suka harbi aƙalla mutune 12 daga cikin masu zanga-zangar a wajen biyan kuɗin shiga na titin Lekki da ke Legas. 

Saƙon ya ƙara da cewa: “Da dama daga cikin mutanen da matasan da suka yi zanga-zangar suna yiwa Peter Obi ƴaƙin neman zaɓen zama shugaban ƙasa ne. Dukkansu, babu wanda baya ciki.”

Najeriya na shirin gudanar da babban zaɓen ta, don zaɓen sabon shugaban ƙasa da mataimakinsa, da kuma ƴan majalisar dattawa da ta wakilai, a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023. 

Za’a iya ganin saƙonnin a Facebook a nan, nan, nan, nan, nan da kuma nan

Da gaske Muhammed ya ce Obi ne ƙashin bayan zanga-zangar #EndSARS? Mun bincika. 

Lai_Peter

Ma’aikatar ta ƙaryata da’awar

Saƙon bai bayyana lokaci da wajen da Mohammed yayi furucin ba. Wannan na daga cikin alamomin da ke nuna cewa da’awar ta ƙarya ce.

Babu kuma wani sahihin gidan jaridar Najeriya da ya kawo rahoton hakan. Idan har ministan yayi irin wannan babban zargi, da tabbas ya zama kanun labarai. 

Bamu samu wata hujja da ta nuna wata sanarwa akan furucin ba a shafin yanar gizo na ma’aikatar yaɗa labarai ko shafin su na kafafen sada zumunta

A watan Yuli, ma’aikatar ta wallafa hoton allon waya na mafi tsayi daga cikin saƙonnin a sahihin shafin ta na Tiwita tare da tambarin dake cewa “BOGI” akan rubutun. Sun rubuta kamar haka: “#JAN HANKALI AKAN LABARAN BOGI!”

Yayin da zaɓen Najeriya na 2023 ke gabatowa, Africa Check na samun yawaitar kalamai da tsokaci na ƙarya da ake danganta su ga jiga-jigan ƴan siyasa. Wannan ka iya kawo matsala ga muhawarar siyasa ta yanar gizo da ta zahiri, ya kuma ragewa masu zaɓe damar zaɓen wanda suke da cikakken sani a kai.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.