Back to Africa Check

‘Mutuwar farat’ ɗaya bata cikin ‘cututtukan da ke biyo bayan anyi’ allurar rigakafin Covid- fastar ta ƙarya ce ba daga gwamnatin Ireland ta ke ba

Hoton ruwan ɗorawar fasta wadda ke da take kamar haka “Coronavirus COVID-19 ALERT” wato jan hankali akan Coronavirus Covid-19, fastar ta kuma jero cututtakan bayan anyi allurar rigakafin da “ba’a cika samu ba”, an rarraba hoton a ƙalla sau dubu a Facebook, har ma a Afrika ta Kudu. 

Jerin cututtakan sun fara da “ciwon kai”, wanda zai cigaba da tsananta har ya kai ga “mutuwa farat ɗaya”.

Fastar na ɗauke da tambarin gwamnatin ƙasar Ireland, tana kuma cewa mutune su kai rahoton ciwon bayan anyi allurar rigakafin ga hukumar kula da ababen kiwon lafiya ta ƙasar wato HPRA. 

Tayi kama da irin fastocin da hukumar lafiya ta ƙasa wato Health Service Executive (HSE) ta ke rabawa mai bayani akan Covid

Amma ta gaskiya ce? Yanzu da ake da alluran rigakafin Covid da aka amince da su da dama, ko ɗaya daga ciki na jawo ”mutuwar farat ɗaya”?

poster_fake

Fastar na ɗaya daga cikin fastocin ƙarya

Abubuwa da dama da basu dace ba sun bayyana cewa fastar ta ƙarya ce.

Bata gama cike irin tsarin da HSE suke yiwa fastar su ba. Nasu na rubuta shawara ga kiwon lafiya wato “Public Health Advice”- ba jan hankali “ALERT” ba. 

Fastocin HSE na amfani da tambarin su ba tambarin gwamnatin ƙasar Ireland ba. Sannan kuma tambarin ma bai yi dai-dai dana gwamnatin ƙasar ba, an sauya shi inda ya ce “jama’ar Ireland”. 

Lokacin da kamfanin dillancin labarai na AP suka tantance fastar, mai magana da yawun HPRA ya ce, “wannan ba abun da HPRA ta fitar ba ne ko wani saƙo daga hukumar lafiya ta Health Service Executive”. 

Bolivia Verfica, wadda ke ƙasar Bolivia da ke Kudancin Amurka sun tantance fastar. Sannan kuma Journal, wani kamfani watsa labarai da ke Ireland sun taɓa tantance wata fastar ƙarya da ta kwafi irin tsarin HSE don yaɗa labaran ƙarya.

Ko “ciwo bayan anyi” allurar rigakafin Covid-19 zai iya jawo “mutuwar farat ɗaya”?

Alluran rigakafin basu da illa, suna hana kamuwa da Covid-19 

Mahukunta a ƙasashe sun amince da amfani da jimlar alluran rigakafin Covid-19 guda 23 a faɗin duniya. 

Duk sun bi tsarin da ya dace don tabbatar da rashin illar su, da kuma ganin sun bada kariya daga cutar. (A duba kundun bayanai na Africa Check akan yadda ake amincewa da magunguna da alluran rigakafin a Afrika ta Kudu, Najeriya da Kenya.)

Hanyoyin da aka bi sun haɗa da manyan gwaje-gwaje. Bayan an amince da alluran rigakafin, ana cigaba da bibiyar su don tabbatar da basu bayar da wata illa ba. 

Kuma cututtakan da ake iya samu bayan anyi kowacce allurar rigakafi daban ne.. 

“Da dama daga cututtakan da ake iya yi bayan alluran rigakafin Covid-19 sun haɗa da zazzaɓi ko zogi ko kuma wajen da akayi allurar yayi ja,” cewar Hukumar kula da cututtaka masu yaɗuwa ta Afrika ta Kudu (NICD). “Sauran cututtakan sun haɗa da zazzaɓi mai zafi, kasala, ciwon kai, ciwon jiki, ƙuraje a wajen da akayi allurar, makyarkyata da gudawa mara yawa.”

Waɗannan cututtaka basa tsananta kuma basa wuce ƴan kwanaki. NICD ta bada gargaɗin cewa matsanantan cututtaka bayan anyi allurar - sun haɗa da rashin lafiyar da wani abu da jiki baya so ke haddasawa, wanda kuma kowacce irin allurar rigakafi zata iya jawowa- an taba kawo rahoton hakan. Amma wannan ba kasafai ya ke faruwa ba. 

A cikin wani ɗan littafi da babu kamar sa a shafin yanar gizo na HSE a Ireland, littafin ya ce: “Kamar kowanne magani, alluran rigakafi na iya sa wani ciwo. Yawancin wannan na zuwa daga mai sauƙi zuwa matsakaita, na kuma gajeren lokaci, kuma ba kowa ne ke samun su ba.”

HSE - da kuma hukumomin lafiya a duk faɗin duniya - suna ba da shawarar cewa allurar rigakafi itace hanya mafi kyau ga jama’a don kare kansu daga Covid-19.”

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.