Back to Africa Check

Shugaban jam’iyya mai mulki APC Adamu bai ce hukumar zaɓe ba zata iya hana yara zaɓe ba

A TAƘAICE: Babu hujjar cewa Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar All Progressives Party, ya ce hukumar zaɓe bata da “ƙarfin da” zata hana ƴan ƙasa da shekaru 18 yin zaɓe, ko cewar su ne “waɗanda ke da ƴancin yin zaɓe”.

Wani babban ɗan siyasa ya ce, hukumar zaɓen Najeriya “bata da ikon” hana ƴan ƙasa da shekaru 18 yin zaɓe a zaɓen ƙasa mai zuwa. 

Wannan na cikin wasu kalamai da ke ta yawo a Facebook tun farkon watan Janairun 2023. 

“INEC ba ta da ƙarfin da zata hana waɗanda shekarun su basu kai ba yin zaɓe, duk zasu kaɗa kuri’a a matsayin su na ƴan ƙasa masu ƴancin yin zaɓe,” a cewar kalaman.

An alaƙanta kalaman ga “shugaban APC”. Ana nufin Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar All Progressives congress.

Ƴan Najeriya na shirin zaɓen sabon shugaban ƙasa, da gwamnonin jihohi da ƴan majalisa, a watannin Fabrairu da Maris. 

A cewar Inec, wato hukumar zaɓe mai zamankanta ta ƙasa, ƴan ƙasar da ke ƙasa da shekarun da aka amince ayi zaɓe na 18, ba za’a barsu su yi rijistar zaɓe, yin zaɓe ko kaɗa kuri’a ba.

Shin Adamu ya faɗi hakan? Mun bincika. 

APCQuote_False

Babu labaran da ya kawo rahoton wannan sanarawa mai tunzurarwa

Furucin bai nuna waje da lokacin da Adamu ya faɗa ba. 

Babu kuma wani gidan jaridar da ya ruwaito shi yana faɗar wani abu makamancin “yin zaɓen waɗanda shekarun su basu isa yin zaɓen ba”.

Idan da Adamu yayi wannan sanarwa mai tunzurarwa da an samu sahihan gidajen jaridar da suka ruwaito. 

Kalaman ƙarya ne.

A tsarin dokoki da hanyoyin yin zaɓe na Inec, akwai hukunci ga waɗanda shekarunsu basu kai ba, ƴan ƙasar waje, ko masu zuwa da sunan wani don yin zaɓe. Ba kawai za’a hana su yin zaɓen ba ne, za’a iya kamasu a kuma gurfanar da su gaban shari’a.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.