Back to Africa Check

Shugaban ƙasa Buhari bai ce kaiwa ƴan bindiga farmaki a matsayin kare kai laifi ne

Wai shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ka re kai daga ƴan bindiga laifi ne? 

Abunda wani saƙo da ke yawo a Facebook tun watan Agustan 2021 ya ruwaito shugaban ƙasar na cewa: “ A dokar ƙasa kaiwa ƴan bindiga farmaki da sunan ka re kai laifi ne, kar a kuskura a gwada yi.”

An wallafa a shafin “I stand with PDP” na Facebook, amma tuni an cire rubutun. PDP itace jam’iyyar da aka fi sani da Peoples Democratic Party, babbar jam’iyyar da ke hamayya da jam’iyyar Buhari mai mulki a yanzu ta All Progressive Congress.

Fitattun masu laifi, waɗanda aka sani da ƴan bindiga, sun addabi yamma maso arewa da tsakiyar Najeriya tsahon shekaru. Wani rahoto da BBC ta fitar a kwanannan ya bayyana matsalar a matsayin: “Gungun ƙungiyar ƴan bindiga akan babura na addabar yankin, suna sace dabbobi, garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa, kashe duk wanda yayi fito na fito da su, suna kuma sawa manoma haraji- wadda hanya ce ta samun maƙudan ƙudi.”

A watan Agusta, gungun ƴan bindiga suka afka Nigeria Defence Academy, wadda jami’ar sojoji ce da ke horar da sojoji dake jihar Kaduna a arewacin Najeriya. Aka kashe sojoji biyu, aka sace ɗaya, sannan aka yiwa da dama rauni.

Amma Buhari yace kaiwa ƴan bindiga farmaki don kare kai laifi ne?

Buhari_quote

‘A kawar da duk ƴan bindiga’

Buhari ya sha shan alwashin kawar da matsalar rashin tsaro da ƴan bindiga ke haifarwa. Idan dai har ya ce mutunen da ke kare kansu daga ƴan bindiga laifi sukeyi, da hakan ya zama muhimmin labari a ƙasar. Amma babu wata kafar yaɗa labarai da ta ruwaito cewa ya faɗi hakan. 

Akwai rahotanni da dama na shugaban ƙasar yana bayyana bakin ciki da ɓacin ransa bisa kashe ƴan Najeriya da ƴan bindiga ke yi. Yayi kuma barazanar rushe duk masu laifin, ya kuma faɗa a Twita cewa: “Duk ƴan bindiga za’a binciko su a kuma kawar da su. Najeriya na buƙatar kasancewa cikin zaman lafiya da tsaro, kuma ba zamu fasa ba sai mu tabbatar da hakan.

A watan Satumba, an ruwaito cewa ya umarci ministan tsaro Bashir Magashi da shugabannin sauran hukumomin tsaro da su “kawo ƙarshen duk wani nau’i na rashin tsaro” a Najeriya.

Waccan magana da aka ce yayi ƙarya ce.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.