Back to Africa Check

Shugaban ƙasar Ghana Akufo-Addo bai cewa ɗan takarar shugaban ƙasar Najeriya Tinubu ya ajiye takara ya bawa abokin hamayyarsa Obi ‘dama’ ba

Shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo ya shigo harkokin siyasar Najeriya bayan ya bawa ɗan takara Bola Tinubu shawarar bawa abokin hamayyarsa Peter Obi hanya. A cewar wasu saƙonni da ke yawo a Facebook tun ƙarshen watan Yunin 2022. 

“A bawa Peter Obi dama, ka tafi ka nemi lafiyar ka- shugaban ƙasar Ghana ya rubutawa Tinubu,” wani nau’i na saƙon ke cewa. Za’a iya ganin wasu nau’ikan saƙon a nan, nan, nan da kuma nan

Za’a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023. Tinubu, mai shekaru 70, shine ɗan takara daga jam’iyyar All Progressive Congress, yayin da Obi, mai shekaru 61, yana takara daga jam’iyyar Labour

Ƙasar Ghana ta na yammacin Africa. Shin shugaban ƙasarta ya rubutawa Tinubu cewar ya bawa Obi “dama” shi kuma ya je don neman magani? Mun bincika. 

Ghana _President

‘Gaba ɗaya ƙarya ce da kuma ɓarna’

Saƙon bai bayyana cikakken bayanin lokacin da Akufo-Addo ya rubutawa Tinubu wasiƙar ba. Babu kuma rahoton wata wasiƙa daga sahihan kafafen yaɗa labarai na gida da na waje, wanda tilas a samu hakan idan da ace da gaske anyi rubutun. 

A ranar 9 ga watan Agusta, Akufo-Addo ya wallafa wani saƙon hoton allon waya na wasu saƙonni a sahihin shafinsa na Tiwita, aka kuma saka tambarin cewa “BOGI NE”. 

A jerin saƙonnin Tiwita guda uku, ya bayyana da’awar a matsayin mai “tayar da hankali”, sannan kuma “gaba ɗayanta ƙarya ce da kuma ɓarna, wacce babu alamun gaskiya a tattare da ita.”

“Ban rubuta wata wasiƙa ga jigon APC ba, ba ni kuma da shirin yi. Ghana da Najeriya na da kyakkyawar alaƙa ta shekaru, ba kuma zai zama ni ne zan shiga al’amuran cikin gida ko na siyasar Najeriyar ba,” Akufo-Addo ya rubuta,

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.