A TAƘAICE: A shekarar 2023, kuɗin Najeriya ya fuskanci matsaloli, kama daga ƙarancinsa zuwa faɗuwar da yayi a kasuwar duniya. Iƙirarin cewa Tinubu ya maye gurbin Nairar da dala ƙarya ne.
A shekarar 2022 aka sauya fasalin Nairar Najeriya, a ƙoƙarin ganin cewa an yaƙi jabun kuɗi da kuma ta’addanci, inda hakan ya jawo matsalar ƙarancin kuɗin da aka fuskanta a watan Fabrairun 2023.
Nairar tayi matsananciyar faɗuwa a kasuwar duniya, don haka a ƙoƙarin ganin an farfaɗo da darajarta shugaba Bola Tinubu ya mayar da chanjin kuɗi ya koma da daraja ta bai ɗaya.
Sai dai a kwana-kwanan nan matsalar musayar kuɗi ta ƙaru yayin da darajar naira ke ta cigaba da faɗuwa.
Dangane da haka ne ake ta yaɗa wani bidiyo a Facebook a Najeriya da ke iƙirarin cewa Tinubu na shirin sauya kuɗin Najeriya zuwa dala.
Bidiyon na da taken: “Najeriya na shirin kawar da Naira, zata fara amfani da dala. Daga Shugaba Tinubu. Ni ɗan aike ne kawai, kar ku kashe ɗan aike.”
Makamanciyar da’awar ta fito a Facebook a nan, nan da nan.
Shin bidiyon Tinubu ne ya ke bayyana niyyar sa ta sauya kuɗin ƙasa zuwa daloli? Mun bincika.

An sauya bidiyon da ke ta yaɗuwa
Bidiyon ya nuna mai gabatar da shirye-shirye na gidan talabijin na Arise News Ojy Okpe, amma daga bisani a wajen da shugaba Tinubu ya ke cewa ƙasar nan zata bar kuɗin naira, daga gani an san cewa sauya bidiyon akayi.
Yadda laɓɓan mai gabatarwar da na shugaban ƙasar ke motsi basuyi dai-dai da abun da ake cewa suna faɗa a bidiyon ba.
Arise News sun fitar da sanarwa nesantar da kansu daga bidiyon a shafin su na X (Twitter a da), sanarwar na cewa bidiyon aikin masu tallata labaran ƙarya ne, sun kuma haɗa sanarwar da sikirinshot na bidiyon tare da rattaba tambarin “FAKE”.
Sanawar na cewa: “Arise News na matuƙar nesanta kanta da wannan MATSANANCIN BIDIYON ƘARYA da ke yawo a kafafen sada zumunta ana kwaikwayon mai gabatar da shirin What’s Trending Ojy Okpe”.
Ba mu kuma samu wani sahihin gidan jaridar gida da waje da ya ruwaito shugaban ƙasar na faɗar hakan ba. Idan da shugaban ƙasar ya faɗi hakan da ya zama kanun labarai.
Ku karanta hanyoyin gane manyan bidiyon ƙarya da bidiyon da aka cire su daga muhallinsu, don ku gano su ku kuma kiyaye faɗawa tarkon su.
Republish our content for free
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment