Back to Africa Check

Tafarnuwa bata maganin chlamydia- ƙwayar cutar da ake yaɗawa ta hanyar jima’i, wadda zata iya jawo mummunar illa, don haka a je a sha magungunan da likita zai bayar.

Chlamydia cuta ce da ake yaɗata ta hanyar jima’i wadda ke kama maza da mata. Ƙwayar bakteriya chamdydia trachomatus ke haddasa ta, wadda idan ba’a yi maganin ta ba zata iya jawo matsala a lafiyar jiki nan gaba. 

Amma wani saƙo da aka wallafa a wani shafin Facebook a Najeriya da ke tallata magungunan gargajiya, yayi iƙirarin cewa cin tafarnuwa kafin a ci komai zai magance chlamydia.

Saƙon na cewa: “ A ci tafarnuwa guda 2 zuwa 4 da safe kafin a ci komai na tsahon wata 1, sai a je ayi gwaji don tabbatar cewa babu cutar chlamydia. Wannan magani na da matuƙar inganci.”

 Shin wannan maganin zai yi maganin chlamydia? Mun bincika.

Chlamydia_incorrect

 

Ya zaku san kuna ɗauke da chlamydia?

A cewar asibiti mallakar Amurka, wato Mayo Clinic, alamun cewa ana ɗauke da ƙwayar cutar Chlamydia trachomatus, sun haɗa da:

  • Fitsari mai zafi
  • Fitar ruwa daga gaban mace
  • Fitar ruwa daga azzakarin namiji
  • Jin zafi yayin saduwa ga mata
  • Zubar jini tsakanin al’ada da kuma lokacin saduwa
  • Zafi a ƴa’ƴan maraina ga maza

Idan cutar ta daɗe zata jawo matsalar da zata dawwama.

“ Cutar chlamydia tana shafar idanu, har ta kan jawo makanta, tana kuma illata hanyoyin fitar fitsari, idan ba’ayi maganin ta akan lokaci ba,” Ademola Popoola, babban malami kuma ƙwararren likitan mafitsara, ya shaidawa Africa Check.

Maganin cutar cikin sauƙi da magunguna masu kashe ƙwayar bakteriya

“ Babban magani shine shan magungunan kashe ƙwayar cutar bakteriya,” Popoola ya ƙara.

Hukumar kiwon lafiya ta Britaniya ta bada shawara makamanciyar wannan. 

“ Za’a iya maganin Chlamydia da magungunan kashe ƙwayar cutar bakteriya,” shawarar su akan cututtaka ta ambata.

Ana buƙatar masu ɗauke da cutar da su ƙauracewa saduwa na tsahon kwanaki bakwai bayan an fara shan magani, don taƙaita yaɗuwar cutar. Dole a sha duk magungunan da aka buƙaci mutum ya sha don samun waraka daga cutar.”

Cin tafarnuwa kafin a ci komai bai zai warkar da cutar chlamydia ba. A je a ga likita. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.