“Ubangiji ne kawai zai iya hana ni zama shugaban ƙasa- Tinubu,” a cewar wani rubutu a Facebook da aka wallafa a ranar 4 ga Disemba 2021.
“Asiwaju Bola Tinubu, jagorar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) na ƙasa, ya ce yana sane da cewa ƴan Najeriya a fusace suke bisa gazawar masu mulkin ƙasar, da kuma gazawar gwamnatin ƙasar wajen ka sa inganta rayuwar ƴan ƙasar.”
Tinubu dai tsohon gwamnan jihar Lagos ne da ta ke kudu masu yammacin Najeriya kuma tsohon ɗan majalisar dattawa ne.
Tun dai bayan ya bar muƙaminsa ya ke ta harkar siyasa, inda ya ke wa jam’iyyar APC yaƙin neman a zaɓe ta, a matsayinsa na jagorar jam’iyyar All Progressive Congress na ƙasa.
Amma Tinubun ya faɗi waɗannan kalamai?
Babu hujjar da ta tabbatar da Tinubun ya faɗi hakan
Rubutun bai nuna waje da lokacin da Tinubun ya faɗi hakan ba.
Irin waɗannan kalamai idan dai har an faɗe su suna kasancewa kanun labarai a duk kafafen watsa labaran Najeriya. Sai dai babu wata ingantacciyar kafar watsa labarai da ta ruwaito hakan.
Duk da cewa akwai ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓe da suke nuna goyan bayan su ga ɗan siyasar, amma dai bai taɓa magana akan hakan ba ko bayyana sha'awarsa na neman wata kujerar mulki.
Saƙon na ƙarya ne.
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment