Back to Africa Check

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya a mulkin soja Babangida bai wallafa goyan bayan Obasanjo na tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa Obi a shafin Tiwita ba

A TAƘAICE: Wani saƙon Tiwita da ke ta yawo a Facebook na cewa tsohon shugaban ƙasar Najeriya a mulki soja Ibrahim Babangida ya ce, ya girmama tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo bisa tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar Labour Peter Obi. Sai dai saƙon ya fito ne daga wani shafin Tiwita na bogi. 

 

“Janar Olusegun Obasanjo zai kasance dattijon kirki na har abada kuma shugaban sojoji,” a cewar wani saƙon Tiwita da aka wallafa a ranar 3 ga watan Janairun 2023. 

“Babu wani soja da ke kan aiki da ya shiga aikin soja kafin shekarar 1982. Inda a lokacin Obasanjo tuni ya gama aikin soja. Ina girmama shi sosai akan abun da ya tsayar.” 

Saƙon na Tiwita ya fito ne daga wani asusun shafin Tiwita mai suna “Ibrahim B. Babangida” wanda ke amfani da sunan @General_Ibbro.

Ibrahim Babangida tsohon shugaban sojoji ne wanda kuma tsohon shugaban ƙasar Najeriya ne da yayi mulki a shekarar 1985 zuwa 1993. 

Olusegun Obasanjo shugaban ƙasar Najeriya ne daga shekarar 1999 zuwa 2007, kuma ya kasance mai faɗa aji a harkokin siyasar ƙasar. A ranar 1 ga watan Janairu ya tsayar da Peter Obi daga jam’iyyar Labour a matsayin ɗan takarar sa na shugaban ƙasa a zaɓen ƙasar mai zuwa, wanda za’ayi ranar 25 ga watan Fabrairu. 

An wallafa hoton allon waya da aka dauka na saƙon na Tiwita a Facebook a nan, nan, nan da nan

Da gaske Babangida ya aika saƙon na Tiwita, cewa yana girmama Obasanjo saboda tsayar da Obi? Mun bincika. 

Babangida_False

‘Waɗanda suke da hannu wajen wallafa saƙon Tiwitan maƙaryata ne’


Bayanan da ke shafin @General Ibbro na nuna shafin na bogi ne. Amma hakan bai hana mutane yin tsokaci da rarraba saƙon ba.

A lokuta da dama Babangida ya fito ya sanar da cewa shi fa bashi da shafi a kafafen sada zumunta. 

A shekarar 2018, Babangida ya keɓe sanarwa cewar kafar sada zumunta ta Tiwita da ke amfani da sunansa, sunayi ne don a soke shi. 

Kassim Afegbua, mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar ya ƙaryata da’awar da ke cewa Babangida ya tsayar da Obi. 

“Ba gaskiya ba ne. Ayi watsi da rahoton cewa ya tsayar. IBB bashi da shafin Tiwita,” kamar yadda ya shaidawa Nigerian Tribune.

“Idan ma har zai yi magana, zai yi ne ta sanarwar da ya sawa hannu bata Tiwita ba. Waɗanda ke da hannu wajen wallafa saƙon Tiwitan maƙaryata ne.”

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.