Back to Africa Check

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Obasanjo bai buƙaci ƴan Najeriya da su samu bindigogi don kare kansu ba

“Zaɓen 2023: Kowa ya shirya, Fulani sun mamaye Najeriya. Sun gane yanzu cewa zasu faɗi akan Peter Obi, ku samo bindigogi babu mai kare ku- Obasanjo,” saƙon na Facebook ya ke cewa tsohon shugaban ƙasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce. 

Fulani wata ƙabila ce da ke warwatse a wurare da dama na Africa. Su na nan da dama a Najeriya, Mali, Guinea, Senegal da Nijar. 

Obi ɗan siyasa ne a Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party. Obasanjo yayi shugabancin Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar People's Democratic Party (PDP). 

Obi shine wanda ake ta yaɗa cewa shine a matsayin zaɓi “na uku mafi ƙarfi” bayan ƴan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyya mai mulki ta All Progressive Congress party da jam’iyyar adawa ta PDP.

Mafi akasarin Fulani Musulmi ne, kuma an san su da kiwon shanu da dabbobin gida. Sai dai, a cikin su akwai mayaƙan da ke da alhakin kai hare-hare akan al’ummomi a faɗin ƙasar.

An sake yaɗa wata da’awar a kafafen sada zumunta cewa wasu Fulani na shirin karɓe Najeriya don mai da ita ƙasar Musulunchi.

Arewacin Najeriya na cike da Musulmi yayin da Kiristoci da dama na zaune a Kudu. 

Wannan da’awar ta ranar 4 ga watan Yuli an sake maimaitata a wasu saƙonnin Facebook da Tiwita

Shin Obasanjo yayi wannan magana da zata iya tayar da hankalin ƙasa, ta zama barazana ga tsaro

Obasanjo_False

Tsohon shugaban ƙasar bai faɗi wani abu makamancin haka ba

Ainihin saƙon bai bayyana cikakken waje da lokacin da Obasanjo yayi maganar ba. 

Babu kuma wani sahihin gidan jarida da ya ruwaito Obasanjon yayi maganar, ko maganar da ta danganci cewa ƴan Najeriya su ɗauki bindigogi.

Irin wannan magana dole ace sahihan gidajen jarida sun ruwaito ta, kasancewar Obasanjo mutum ne da ake ganin girman sa a duniya, wanda kuma har yanzu ake damawa da shi a siyasar Najeriya. 

Yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa, Africa Check na ƙara cin karo da bayanai ko kalamai na ƙarya da ake danganta su ga ƴan siyasa. Wannan zai iya ɓata muhawarar siyasa a yanar gizo da kuma a zahiri, ya kuma ragewa masu zaɓe damar zaɓen waɗanda suke da cikakken bayani akan su.

Republish our content for free

Please complete this form to receive the HTML sharing code.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.