A TAƘAICE: An tabbatar da cewa jita-jitar da ke yaɗuwa a tsakiyar watan Oktoba 2023 cewa tsohon shugaban ƙasar Najeriya a mulkin soja Janar Yakubu Gowon ya mutu ƙarya ce
“Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Janar Yakubu Gowon ya mutu yana da shekaru 89”, cewar wani rubutu a Facebook.
Rubutun da aka yi shi a ranar 23 ga watan Oktoba 2023, na iƙirarin cewa tsohon shugaban ƙasa a mulki soja, kuma janar na soja mai ritaya ya mutu yana da shekaru 89.
Rubutun ya samu sama da mutane 100 da suka so shi suka kuma yi tsokaci, an samu kuma ra’ayi daban-daban daga masu amfani da Facebook. Shin hakan gaskiya ne?

Gowon bai mutu ba
An haifi Yakubu Gowon a tsakiyar jihar Plateau a shekarar 1934. Yayi karatu a jihar da a yanzu aka sa ni da Kaduna, sannan ya fara aiki a matsayin jami’in soja.
Gowon yayi shugaban ƙasa daga shekarar 1966 zuwa 1975.
Adeyeye Ajayi, mataimaki ga Gowon ya ƙaryata jita-jitar cewa janar ɗin ya mutu.
The Cable sun ruwaito Gowon na cewa “Ina nan dai kuma ƙalau. Ba sauri na ke ba” a wata sanarwa da aka aikawa gidan talabijin na Nigerian Television Authority.
A wani rahoton da Punch ta wallafa, Olorogun Kenneth Gbagi, tsohon ƙaramin ministan ilimi, ya bayyana jita-jitar da ke yawo a matsayin “aikin masu ɓarna”.
Jita-jitar mutuwar Gowon ƙarya ce.
Republish our content for free
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment