Back to Africa Check

Yaƙin Rasha da Ukraine bai jawo ƙasar Biritaniya samun koma baya akan tattalin arzikin ta ba ko haɗa hulɗar mai da Najeriya

Wani saƙo da ke yawo a Facebook yayi iƙirarin cewa yaƙin Ukraine ya jefa Biritaniya cikin koma bayan tattalin arziki. Saƙon ya ƙara da cewa firaiministan Biritaniya Boris Johnson yana ƙokarin ƙulla wata alaƙa da gabas ta tsakiya da Najeriya- “akan hauhawar rikicin mai”.

Saƙon na cewa: “Biritaniya na cikin rikicin tattalin arziki, yaƙi a Ukraine.. Boris na ƙulla alaƙa da gabas ta tsakiya don kiyaye Biritaniya daga hauhawar da rikicin mai ke yi. Saboda dalilan da suka danganci tattalin arziƙi, ‘GB Incorporated’ zasu haɗu da Najeriya don duba mu su kasuwar mai a kuma cigaba da rikicin jinƙan yankin Biafra.”

Saƙon na da kwanan watan da ya nuna 21 ga watan Maris 2022, an kuma rarraba shi sama da sau 647

Biafra na nufin kudu maso gabashin Najeriya inda ake ta neman mai da ita ƙasa ta daban, wato jamhuriyar Biafra. Jamhuriyar dai tun shekarar 1967 zuwa 1970 ta ke, hakan kuma ya haddasa yaƙin basasa a Najeriya.

Amma Biritaniya na cikin koma bayan tattalin arziki? Kuma rikicin Ukraine ya sa Biritaniya neman Najeriya saboda buƙatar mai? 

Russia_fuel

Biritaniya bata fuskanci koma baya a tattalin arziki ba, har zuwa Maris 2022

Ƙasa na fuskantar koma baya a tattalin arziki ne idan ta samu raguwar hauhawar farashin kayan cikin gida har sau biyu a jere(GDP), a cewar Asusun Ba da Lamuni na Duniya(IMF). GDP na nufin darajar dukkan kayayyaki da ayyukan da ake samarwa a ƙasa. 

Babu wata hujja a bayyane da ta nuna cewa Biritaniya ta samu koma baya a tattalin arzikin ta, har kawo watan Maris 2022. 

Adadin GDP da aka wallafa na kwana kwanan nan wanda ofishin tattalin arzikin Biritaniya ya fitar ya bada bayanin watan Janairun 2022 ne. A watan kuwa GDP ya hau da kashi 0.8%, kuma ƙaruwa ya ke tun daga watan da ya gabaci watan da aka fitar da adadin. Ofishin zai fitar da adadin watan Fabrairu a ranar 11 ga watan Afirilu.

A nazarin da IMF ta fitar a cikin watan Fabrairu ya nuna cewa tattalin arzikin  Biritaniya ya farfaɗo- daga annobar Covid, sannan duk da fitar Biritaniya daga ƙungiyar haɗa kan ƙasashen turai- tattalin arzikin ya samu cigaba fiye da yadda ake zato. Yana kuma nuna cewa an kusa cimma wa’adin da ake buƙata 

Hukumar tattalin arziki da bincike akan zamantakewa ta Biritaniya tayi wani hasashe a watan Maris cewa ƙasar zata iya shiga faɗuwar tattalin arziki na tsakiya kashi na biyu na shekarar 2022 idan farashin makamashi ya cigaba da tsayawa a yadda ya ke. Ta ce sassauƙan tsarin kasafin kuɗi “zai iya hana yiwuwar faɗuwar tattalin arzikin”.

Firaiminista na shirya wasu hanyoyin samun mai

Akwai rahotannin da ke cewa Johnson yayi yunƙurin hada wata alaƙa ta makamashi da ƙasashen gabas ta tsakiya, bayan rikicin makamashin da mamayar da Rasha ta yiwa ukraine ya haddasa. 

Amma bamu samu wata hujja da ta nuna cewa firaiministan yayi makamanciyar wannan alaƙa da Najeriya ba. 

Biritaniya bata fuskanci faɗuwar tattalin arziki ba har zuwa watan Maris 2022. Yayin da ta na iya yiwuwa Johnson na zawarcin ƙasashen gabas ta tsakiya masu samar da mai, amma ba zamu ce hakan ne tsakanin sa da Najeriya ba ko kuma akan yanayin da kudu maso gabashin Najeriya ke ciki ba.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.