A TAƘAICE: Rubuce-Rubuce da dama a Facebook na iƙirarin cewa ƴan Najeriya masu sha’awa zasu iya cike neman tallafin rukunin kamfanin Dangote. Ayi watsi da hakan.
“Tallafin karatu na Dangote ga ƴan Najeriya. Ku nema a nan,” saƙon na Facebook ke cewa.
Saƙon na haɗe da wajen da za’a latsa wato link da zai kai mutum wani shafin yanar gizo da masu buƙatar tallafin zasu iya cike izinin nema.
Aliko Dangote shine shugaban rukunin kamfanunnukan Dangote, babban mai samar da siminti, kuma babban mafi girman ɗan kasuwa a Yammacin Afrika.
Mujallar Forbes ta bayyana Dangote a matsayin mutum mafi ƙarfi a Afrika. Mujallar Time kuma tace shine mutum mafi tasiri a duniya.
Shine kuma daraktan gidauniyar Aliko Dangote, wadda ke tallafawa mutane a fannin lafiya da ilimi.
Mun ci karo da makamanciyar da’awar a nan da nan. (A lura: Za’a samu wasu misalan a ƙarshen wannan rahoton.)
Shin ƴan Najeriya zasu iya neman “tallafin karatu na Dangote” ta hanyar amfani da link ɗin da aka samar? Mun bincika.
Babu dangantaka da Dangote
Africa Check ta latsa link ɗin har ya kaimu ga wani shafin yanar gizo mai taken: “Ku fara neman izini.” Yana kuma da wani koren abun latsawa da ke cewa “KU NEMA A NAN” aka kuma bayyana ranar “16 ga watan Yuli, 2024” a matsayin ranar da wa’adin neman tallafin zai cika.
Mun latsa koren wajen latsawar ya kuma kai mu wani shafin yanar gizo na blog mai ɗauke da izinin neman aiki a ƙasar Australia daban-daban da kuma yadda za’a nema.
Mun duba shafin yanar gizo na Dangote da kuma shafukan kafafen sada zumunta na gidauniyar, amma bamuga wani abu makamancin sanarwar neman tallafin ba. Link ɗin na daga cikin abun da wasu mutane keyi don neman masu shiga shafi, don cimma manufar su ta neman a sansu da kuma samun yawan masu shiga shafi.
Don kiyaye kan ku, ku karanta hanyoyin da muka jero muku don kare kai daga zamba a Facebook da yadda zaku iya gano ta.
An samu makamanciyar wannan da’awa a nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan da nan.
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment