Back to Africa Check

Ƴan Najeriya ku kiyayi shafin bogi da ke cewa ku biya N500 don samun damar samun kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke rabawa

A TAƘAICE: Wani shafin Facebook na iƙirarin aikawa ƴan Najeriya kuɗi, yana cewa gwamnatin tarayya ce. Ƴan Najeriya su kiyaye.

 

A watan Yuli 2023, shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu ya bayyana shirin raba N8,000 duk wata na tsahon watanni 6 zuwa ga iyalai miliyan 12, da ake zaton sune mafi talauchi (kwatankwacin US$9.50, a watan Nuwamba na 2023). Wannan na zuwa ne bayan cire tallafin man fetur da akayi a watan Mayu

Shirin ya gamu da ce-ce-ku-ce daga jama’a, suna neman shugaba ƙasa da ya sake duba al’amarin. 

Shafin na Facebook mai suna Federal Government Disbursement Programme yayi iƙirarin cewa masu amfani da shafin zasu iya samun kuɗaɗen ta shafin

Wani rubutu da aka wallafa a ranar 10 ga watan Oktoba, wani ɓangare daga ciki ya ce: “Gwamnatin tarayya na amfani da wannan hanyar wajen yin kira da ganin an yi rabon naira 8,000 ɗin da aka shirya bayarwa a bayyane, wanda kuma aka shirya bayarwa duk wata a matsayin tallafi (na tsohon watanni shida) ga ƴan Najeriya miliyan 60.”

Shafin ya sake yin irin wannan da’awar a nan da nan

Amma hakan ce hanyar da ƴan Najeriya ya kamata suyi rijista ko karɓar tallafin kuɗin da Tinubu yayi alƙawari? Mun bincika. 

GovernmentFund_Scam


Alamun damfara

Shafin yanar gizon da aka danganta da saƙon yana da taken “SHIRIN GWAMNATIN TARAYYA NA RABAWA” sannan ya nuna hoton Tinubu yana rattaba hannu a wani abu. 

Shafin na umartar masu amfani da shi da su bada N500 don samun damar samun kuɗin. Suna kuma tambayar bayanan sirri na mutum da suka haɗa da sunan mutum, email, lambar waya, lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) da kuma jihar asali. 

Ana kuma tambayar bayanan banki. Waɗannan duk alamu ne da ya kamata a kula da su, musamman da aka bada gargaɗin cewa shafin ba zai kasance a asirce ba bayan an buɗe. 

Shafin Facebook da ke saka link ɗin shafin an ƙirƙire shi a ranar 9 ga watan Oktoba 2023. Ma’aikatar jinƙai ce ke da alhakin sabon shirin rabon tallafin, don haka ya kamata ace ƴan Najeriya sun san cewa duk bayanan da suke buƙata zasu samu a sahihin shafin ma’aikatar, ba a wani sabon shafi da wasu suka ƙirƙira ba. Shafin ma’aikatar an ƙirƙire shi a 2019, yana kuma da mabiya har sama da 100,000. 

An ƙaddamar da shirin a watan Oktoba ga waɗanda aka zaɓa

Shugaban ƙasa ya ƙaddamar da shirin aika kuɗi mai ƙa’idoji a ranar 17 ga watan Oktoba. Kuɗin da za’a raba wata-wata ya tashi daga N8,000 duk wata na tsahon watanni shida zuwa N25,000 a wata har tsahon watanni uku. 

Waɗanda zasu amfana da shirin a cewar rahotanni, National Society Safety Nets Coordinating Office ne suka zaɓo su daga rajistar zamantakewa (NSR). Babban aikin ofishin shine samar da tushen samun cikakken bayanan magidanta masu ƙaramin ƙarfi da marasa galihu a Najeriya ta hanyar ƙirƙirar NSR. 

Ba mu samu rahoton cewa mutane zasu iya neman tallafin kai tsaye ba, ko su biya wani kuɗi don su samu ba. Gwamnatin tarayya ta ce zata zaƙulo masu ƙaramin ƙarfin da suka cancanci su samu kuɗin. 

Africa Check ta ƙaryata da’awa makamanciyar wannan a wani shafin a watan Oktoba. Shafin kansa na bogi ne. 


 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.