Back to Africa Check

Yi watsi da saƙon Facebook da ke cewa, gane cutar sikari, Alzheimer’s, cutar Parkinson’s, cutar Covid-19 da ma wasu cututtakan da kan ku

“ Jama’a ga magani na asali,” abun da ke jikin wani hoto da ke yawo a Facebook a Najeriya a watan Nuwambar 2020.

Hoton na ƙunshe da da’awa da dama akan yadda mutum zai gane yana ɗauke da wasu cututtaka.

Rubutun na cewa: “ ku je kan bishiya ku ƙwararo fitsari, idan fitasarin ya jawo tururuwa na bi, ku na da ciwon siga, idan fitsarin ya bushe, kuna da sodiyom da yawa a jiki, idan yana warin nama, kitse yayi muku yawa a jiki, idan kun manta ku kwance mazugin ku kuna da Alzheimer’s, idan kun wuce bishiya baku sani ba kuna da Parkinson’s, idan kun yi fitsari a cikin takalmin ku kuna da matsalar mafitsara ta kunburin frostait, idan ba kwa jin wari ko ƙanshi kuna da Covid-19.”

Masana sunyi gargadin cewa wannan saƙo ba haka abun ya ke, zai kuma iya kai jama’a da shan magani ba tare da umarnin ƙwararru ba.

 

self diagnosis false

 

Cututtaka da yanayinsu sun bambanta 

Cutar sukari nau’i na 1 cuta ce da ke faruwa lokacin da fankiriyas ya gaza samar da isasshen sinadarin insulin a jiki. Cutar sukari nau’i na 2 wanda aka fi sani da kin amsar da insulin, shine lokacin da ƙwayoyin halitta suke ƙin amfani da insulin ko rashin amfani da shi yadda ya kamata.

Alzheimer’s kuma cuta ce da ta shafi ƙwaƙwalwa wadda bata da magani. Tana sa ƙwaƙwalwa ta ƙanƙance kuma ƙwayoyin halitta ma su mace. Ana gane masu ɗauke da cutar ta hanyar gwaje gwaje a asibiti, kamar gwajin fitsari, gwajin jini da gwajin ƙwaƙwalwa da suka haɗa da gwajin tuni, na magance matsala, na mai da kai, na ƙidaya da na harshe.

Cutar Parkinson’s, cuta ce da ta ke shafar jijiyoyi wadda ke jawo tauri ko nawa wajen motsi. Alamunta sun haɗa da magana ba dai dai ba da rawar hannaye. Duk da cutar ka iya tsananta tsahon lokaci ana iya shan magani don shawo kan cutar 

Duk da dai rashin jin ƙanshi da wari na daga cikin alamomin cutar Covid-19, amma wasu cututtaka kan iya haifar da hakan.

‘ Ku je masana su yi muku bincike don gano cutar’ 

Africa Check ta tuntubi Sulayman Kuranga, farfesa a fannin lafiyar mafitsara na jami’ar Ilorin a yammacin Najeriya, don jin ko ya inganta jama’a su yi irin wannan gwajin a gida.

“ Fitsarin da tururuwa ke bi tabbas yana dauke da sukari a cikin sa. Amma kuma zai iya zama ana dauke da ciwon sukari ba tare da sukari ya nuna a cikin fitsari ba. Cutar gonococcal na sa mafitsara ta toshe har  fitsari ya ringa fita ba daidai ba,” farfesan ya ce.

Kuranga ya ce akwai gwajin yawan sodiyom da na yawan kitse, don haka “ marasa lafiya su je asibiti a gwada su”.

Aihanuwa Eregie, farfesa a fannin magunguna kuma ƙwararre wajen kula da cututtukan da suka shafi abubwan da jiki ya ke fitarwa don sarrafa jikin a jami’ar Benin da ke kudu masu yammancin Najeriya, ya shaidawa Africa Check cewa akwai gwaje gwajen cutar sukari da aka amince da su a kimiyyance, “ ta waɗannan gwaje gwaje ne muke gane masu ɗauke da ciwon sukari”.

Mun kuma tuntubi Njideja Okubadejo, farfesa akan lafiyar ƙwaƙwalwa a jami’ar Lagos akan yadda ake gane cututtukan Alzheimer’s da Parkinson’s.

Ta shaida mana cewa:, “ Cututtaka ne da suka shafi ƙwaɗwalwa, yawan shekaru ma na jawo su, amma cutar Parkinson’s zata iya kama matasa ma. Cututtakan na faruwa ne lokacin da wasu ƙwayoyin halitta da ke ƙwaƙwalwa suke fara mutuwa.”

Ta kuma bayyana cewa, duka cututtakan na buƙatar ƙwararru a fannin su duba masu alamun cutar: “ Don haka jama’a su je asibiti don a duba a tabbatar ko suna fama da su.”

Ƙwararru na bada shawara ga duk mai zaton wata matsala a lafiyar sa, ya garzaya wajen likita, maimakon duba kan su a gida ko amfani da abun da bai dace ba.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.