Back to Africa Check

Masanin ƙwayoyin cuta Montagnier bai ce ‘ duk waɗanda aka yiwa allurar rigakafi zasu mutu cikin shekaru biyu’

Shin Luc Montagnier, ƙwararre akan ƙwayoyin cuta ɗan ƙasar Faransa yace duk waɗanda aka yiwa allurar rigakafi zasu mutu cikin shekaru biyu? Wannan rubutu ne da ke ta yawo a WhatsApp, Facebook da Instagram a Najeriya a watan Mayu 2021.

Da dama daga rubutun da ake yaɗawa na nuna hoton Montagnier da taken: “ Duk waɗanda aka yiwa allurar rigakifi zasu mutu cikin shekaru biyu.”

“ Luc Montagnier wanda ya samu lambar yabo ta Nobel ya tabbatar da cewa babu dama mutum ya cigaba da rayuwa bayan ya yi kowacce daga alluran rigakafin,” rubutu da ake fi yaɗawa ke cewa.

“ A wata ganawa da akayi da shi, babban ƙwararre akan ƙwayoyin cuta ya ce: ‘ babu dama, sannan babu magani ga waɗanda suka riga sukayi allurar rigakafin. Mu shirya ƙona gawawwaki.’ Masanin kimiyar ya kuma goyi da bayan da’awowin wasu masana ƙwayoyin cuta bayan yayi nazarin abubuwa da ke ɗauke  acikin alluran rigakafin. Duk zasu mutu daga haɓakar ƙwayoyin kare ƙwayar cuta a jiki. Babu abun da za a kuma cewa.”

Da dama daga rubutukan da ake yaɗawa an alaƙanta su ga wani rubutu a shafin yanar gizo na LifeSiteNews, wanda ke da taƙen: Wanda ya ci lambar yabo ta nobel: Taron llurar rigakafin Covid ‘kuskure ne da ba a amince da shi ba.”

Da gaske Montagnier ya ce duk waɗanda aka yiwa alllurar rigakafi zasu mutu cikin shekaru biyu?

French virologist_false

 

Ƙarya aka alaƙanta masa, ‘ labaran ƙarya aka kwaikwaya’

Wanda aka haifa a ranar 18 ga watan Agusta 1932, Luc Montagnier masanin binciken kimiyyyar ɗan asalin ƙasar Faransa, wanda ya samu tarin nasarori da suka haɗa da lambar yabo ta Nobel a shekarar 2008 akan ilimin sanin halittar ɗan adam da likitanci. Ya kuma jagoranci tawagar masana da suka gano ƙwayar cutar ƙanjamau (HIV) da kuma abun da ke jawo karyewar garkuwar jiki ( Aids)

Rubutun da LifeSiteNews tayi, wanda aka buga ranar 19 ga Mayu, ya ambato wata hira da Montagnier “ wadda gidauniyar RAIR ta ƙasar Amurka suka fassara kuma suka wallafa a jiya.” Gidauniyar ta bayyana kanta a matsayin “ wani yunƙuri don ƙwanto jamhuriyar mu daga mutane da ƙungiyoyin da suka haɗa kai don yaƙi da Amurka, tsarin mulki, iyakokin mu da kare ɗabi’un yahudu da nasara”.

A cewar LifeSiteNews, Montagnier ya kira “ allurar rigakafin cutar korona da abun da ba a yi tunani ba, kuma babban kuskure a tarihi da ke haifar da nau’ikan cutar, wadda ke ta jawo mace-mace daga cutar”. 

“ Babban kuskure ne, ko ba haka ba? Kuskure a kimiyance, a kuma likitance. Kuskure ne da ba za a taɓa amincewa da shi ba,” Sun wallafo Montagnier na cewa. “ Littattafan tarihi zasu tabbatar da haka, saboda allurar rigakafin ke jawo nau’oin cutar.”

Sai dai babu inda rubutun ya ambato Montagnier ya ce duk waɗanda aka yiwa allurar zasu mutu cikin shekaru biyu, ko kuma “ mu shirya ƙona gawawwaki”.

A ranar 27 ga Mayu, LifeSiteNews suka ƙara sabunta rubutun

“ Yayin da LifeSiteNews ta ruwaito abun da Montagnier ya faɗa, wasu masana kimiyya sun yi watsi da rubutun sa, na cewa alluran rigakafin na jawo sababbin nau’ikan cutar,” sabon rubutu ya fara da cewa

Ya kuma ƙare da cewa: “ Abu na biyu shine, Montagnier bai ce duk wanda aka yiwa gwajin  allurar rigakafin Covid-19 ‘zai mutu’ cikin shekaru biyu ba. Wannan maganar an ƙage ta, an danganta masa ita a matsayin labaran ƙarya da ya ke ta bazuwa.”

Ba mu samu wata hujja da ta tabbatar da cewa Montagnier yayi waɗannan kalamai ba.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.