Back to Africa Check

Albasa tana ƙarawa maza ƙarfin jima’i? Masana sun ce ba haka ba ne

A TAƘAICE: Saƙonni a kafafen sada zumunta na bada shawarar cewa cin albasa ɗanya ko shan ruwanta ne sahihin maganin ƙara ƙarfin jima’i. Sai dai hujjojin da suke ka re wannan da’awar kaɗan ne.

Wani rubutu da aka raba a Facebook Najeriya na iƙirarin cewa wai albasa na ƙarawa maza ƙarfin jima’i.

An rarraba wannan da’awa a shafukan Facebook daban-daban. Sun kuma bayyana albasa a matsayin “ɗaya daga cikin mafi girman abinciccikan da ke ƙara ƙarfin maza”. 

Wasu daga cikin rubutun an wallafa su tun watan Juli 2021. 

“Tana taimakawa wajen ƙara ƙarfin sha’awa, tana kuma ƙara ƙarfin sassan jiki da ke da alhakin kula da haihuwa. Albasa na ƙara yawan sinadarin testosterone a jiki, tana kuma taimakawa wajen ƙara ƙarfin jima’i,” rubutun na 27 ga watan Afrilu 2023 ke cewa

Rubutun na bada shawarar cewa “za’a iya cin albasa ɗanya ko ayi ruwanta”, ko a markaɗa. “Ruwan albasar nada ɗaci, don haka a zuƙa a hankali don kar ya taɓa muku tsarin jiki,” rubutun ya ce.

Sinadarin jiki na testosterone, sinadari ne da ke da alhakin kula da jima’i a jikin ɗan adam, kuma yana ayyuka da dama a jiki, kamar kula da haɓɓaka azzakari da ƴaƴan maraina, samar da maniyyi, girman tsokokin jiki, kaurarar harshe lokacin shekarun balaga da kuma samuwar gashin fuska da na gaba. 

Ana samun sinadarin a jikin maza da mata.

Za’a iya haɓɓaka shi da cin wannan abinci mai wari? 


Onion_Incorrect

Shaidun da suka goyin bayan da’awar basu da yawa

Maganar cewa albasa, wadda ta fito daga nau’in itatuwan da aka sa ni da allium, na ƙarawa maza ƙarfin jima’i, ba sabuwar magana ba ce. 

Wasu masu binciken kimiyya sun yi bincike akan tasirin ruwan albasa ga yawan sinadarin testosterone a jikin maza da kuma “halayar saduwa” da samuwar maniyya akan ɓeraye maza. Basu samu cikakkun hujjojin da suka nuna cewa ci ko shan ɗanyar albasa na ƙara sha’awa ba. 

Sulyman Kuranga farfesa akan lafiya mafitsara a jami’ar Ilorin da ke jihar Kwara, a yammacin Najeriya. 

Ya shaidawa Africa Check babu binciken kimiyyar da ya tabbatar ruwan albasa na ƙara sinadarin testosterone a jiki ko ya ƙarawa maza ƙarfin jima’i.

“Babu wata ƙwaƙwarar hujjar da ta goyi bayan hakan”, a cewarsa. 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.