A TAƘAICE: A cewar wasu saƙonnin Facebook, an cire shugaban majalisar dattawan Najeriya. Wannan ba haka ya ke ba, ayi watsi da saƙonnin Facebook da ke iƙirarin hakan.
Wani bidiyo da aka saka a Facebook na iƙirarin cewa an tsige shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio.
Wanda ke magana a bidiyon ya ce yana farinciki da labarin, ya buƙaci mutanen da ke amfani da Facebook da su rarraba saƙon.
Bidiyon na ranar 17 ga watan Satumba na da taken: “Da ɗumi-ɗuminsa: Ƴan majalisar dattawa sun fara shirin #tsige shugaban majalisar Akpabio saboda bin son ran Tinubu maimakon son ran jama’a…”
Tsigewa hanya ce da ake bi don cire shugaban ƙasa ko wani babban jami’i daga ofis, sau tari lokacin da suke fuskantar tahuma da laifi.
Masu amfani da Facebook sama da 100,000 ne suka kalli bidiyon, da kuma tsokaci sama da 1000.
Akwai makamancin saƙon a nan, nan da nan.

Shugaban majalisar ya ƙaryata jita-jitar
An zaɓi Akpabio a matsayin shugaban majalisa ta 10 ranar 13 ga watan Yuni 2023. Bayan zaɓen nasa wasu sanatoci sun shirya yadda zasu tsige shi, su na masu iƙirarin cewa bazai iya aikin da aka dora shi a kai ba.
Babban mai bashi shawara akan yaɗa labarai Eseme Eyiboh, yayi watsi da iƙirarin a matsayin wani abu mara tushe.
Majalisar ma ta musanta da’awar tana mai tabbatar da cewa Akpabio ya da ce da matsayin da ya ke riƙe da shi.
Republish our content for free
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment