Back to Africa Check

Babu hujjar cewa Amurka ta haramtawa shugaban hukumar zaɓe Mahmood Yakubu, gwamna Nyesom Wike da wasu samun izinin shiga ƙasar

A TAKAICE: Jita-jita na cigaba da yaɗuwa akan zaɓen Najeriya na 2023, da kuma su ka akan yadda aka gudanar da zaɓen. Babu wata hujja da ta nuna cewa wani dogon jerin sunayen manyan ƴan Najeriya, waɗanda suka haɗa da shugaban hukumar zaɓen an haramta musu samun izinin shiga Amurka.

Wata da’awa da ake yaɗawa a Facebook Najeriya na cewa, ƙasar Amurka ta haramta bawa shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (Inec), Mahmood Yakubu, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode samun izinin shiga ƙasar.

Rubutun yayi iƙirarin cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, da kuma shugaban kwamitin kula da tasoshi da gareji na jihar Legas, Musilu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo, suna cikin waɗanda aka haramtawa izinin shigar. 

“Shugaban INEC, Alhaji Mahmood Yakubu, Wike, MC Oluomo, FFK, Fayose da wasu ma sun shiga cikin jerin waɗanda aka haramtawa izinin shiga Amurka!” rubutun ke cewa. 

Inec ce ke da alhakin gudanar da zaɓe a Najeriya. 

An soki shugaban hukumar ga me da yadda aka gudanar da babban zaɓe, wanda aka yi a watan Fabrairu da Maris 2023. An yiwa hukumar Inec zarge-zarge da dama. 

An ƙalubalanci nasarar zaɓaɓɓan shugaban ƙasa Bola Tinubu a kotun saurarar ƙararrakin zaɓe daga manyan masu adawa, Atiku Abubakar na jam’iyyar People’s Democratic Party da na jam’iyyar Labour Party Peter Obi

Da’awar na nuna cewa Yakubu da duk waɗanda aka lissafa na cikin jerin waɗanda aka haramtawa izinin shiga Amurka saboda yadda aka gudanar da zaɓe. 

Makamanciyar da’awar ta fito a nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan da nan

Hakan gaskiya ne? Mun bincika. 

Visa ban_False

Babu hujjar da ta tabbatar da da’awar

A watan Junairu 2023 Amurka ta sanar da dakatar da bawa waɗanda suke da hannu wajen yiwa zaɓen Najeriya da aka yi kwana-kwanan nan ‘zagon ƙasa’ takardar izinin shiga ƙasar. 

An yi wannan sanarwar ne kafin babban zaɓen 2023, sannan ba’a ambaci wasu sunaye ba. 

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya sake fitar da wata sanarwa a shafinsa na Tiwita a ranar 14 ga watan May 2023. Yana mai cewa Amurka ta “saka takunkumi akan wasu mutane da suka yiwa tsarin demokaraɗiya zagon ƙasa”.

Sai dai Blinken bai ambaci mutanen ba. 

Africa Check ta tuntuɓi Temitayo Famutimi, ƙwararriya akan yaɗa labarai da ke aiki da ofishin jakadancin Amurka, don tabbatar da ko shugaban Inec da wasu na cikin waɗanda aka haramtawa izini shiga ƙasar Amurka. Har zuwa lokacin da muka wallafa wannan rubutu bamu ji daga gare ta ba, amma zamu sabunta wannan rahoto duk sanda muka ji daga gare ta. 

Binciken da mukayi a shafin sashen yin takardar izinin shiga Amurka na yanar gizo, mallakar gwamnatin Amurka, ba mu samu wata shaida ba akan da’awar. 

Babu kuma wani rahoto a kafafen yaɗa labaran Najeriya cewa Amurkan ta saka takunkumi akan takardar izinin shiga akan shugaban Inec. Da da gaske ne da an fitar da rahoto akan da’awar. 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.