Back to Africa Check

Babu hujjar cewa haɗin ayaba, ƙwai, madara da baikin soda na taimakawa mata samun juna biyu- aje a ga ƙwararru akan lalurar mata

A TAƘAICE: Wani rubutu a Facebook da ke yawo a Najeriya na iƙirarin cewa mace mai neman haihuwa zata haɗa nunanniyar ayaba, ɗanyen ƙwai da madara tayi amfani da su. Ba mu samu wata hujja a kimiyance da ta tabbatar da hakan ba.

Wani bidiyo da aka saka a Facebook a Najeriya na iƙirarin cewa shan haɗin nunanniyar ayaba, ɗanyen ƙwai, madara da baikin soda na taimakawa mata samun juna biyu. 

Bidiyon na haɗe da wani rubutu da ke cewa “Wahalar ɗaukar juna biyu, kasa haihuwa, matsalar fitar ƙwayayen mahaifa, ku gwada wannan yana da kyau kuma yana aiki.”

Mai magana a bidiyon na cewa, ayabar ta kasance ta nuna, sannan aka bayyana amfanin su. Ta kuma bawa jama’a shawarar sake shan wannan haɗi bayan watanni uku. 

An kalli bidiyon fiye da sau 84,000. An kuma yi tsokacin godiya da kuma tambayoyi. 

An yi da’awa irin wannan a nan, nan da nan

A shekarar 2019, Africa Check ta ƙaryata irin wannan da’awar. A lokacin wani ƙwararren likitan kula da samun haihuwa ya shaida mana cewa haɗin madara, ƙwai, ayaba da baikin soda basu da tasiri akan haihuwa.

Wannan haɗin zai taimakawa mata samun juna biyu? Mun duba yiwuwar hakan

mixtureinfertility_false

Aje a ga ƙwararrun likitocin mata, Farfesa ya ce

Africa Check ta tuntuɓi Ishaq Abdul, Farfesa akan lalurar mata da masu juna biyu a jami’ar Ilorin akan haɗin da kuma ko haɗin zai taimakawa mata wajen samun juna biyu. 

Ya ce akwai abubuwa da dama da ke jawo matsalolar rashin haihuwa a kimiyance, kuma bai taɓa cin karo da wani bincike akan wannan haɗi ba. 

“A matsayin mu na likitoci masu kula da lalurorin mata, muna yin tambayoyin da suka dace, muna duba marasa lafiya, muna bunciken da ya dace, sannan muyi amfani da sakamakon binciken don gano musabbabin matsala da kuma bada taimakon da ya dace don magance matsala,” ya ƙara da cewa. 

Sannan ya bawa masu son ɗaukar juna biyu shawarar ganin ƙwararrun likitocin mata. 


 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.