Back to Africa Check

Ɗan takarar shugaban ƙasar Najeriya Tinubu bai ce zai miƙa mulki ga ‘ɗan ƙabilar Igbo ba’

Wani saƙo a Facebook na iƙirarin cewa Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar All Progressive Congress(APC) a zaɓen Najeriya na shekarar 2023, ya ce zai miƙa mulki ga ɗan ƙabilar Igbo bayan ya gama wa’adin shekaru takwas yana shugabancin ƙasar.

“Zan miƙa mulki ga ɗan ƙabilar Igbo bayan na yi shekaru takwas ina mulki,” saƙon ya ce Tinubu na cewa. 

Tinubu, wanda yayi gwamnan jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya lashe zaɓen zama ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jami’iyyar APC. Shi zai riƙe tutar jami’iyyar a shekarar 2023.

Ƙabilar Igbo na zaune ne a Kudancin Najeriya. Tun bayan dawowar demokaraɗiya a shekarar 1999, al’ummar Igbo basu riƙe shugabancin ƙasar nan ba.

An rarraba saƙon sama da sau 800, sannan ya samu tsokaci har guda 12,000.

Sannan an cigaba da yaɗa da’awar a wasu saƙonnin a wasu shafukan Facebook: a nan da nan

Tinubun ya ce zai miƙa mulki ga ƴan ƙabilar Igbo bayan yayi shugabancin ƙasa na shekaru takwas?

Tinubu_False

‘A’a, bai ce haka ba’

Saƙon bai bada cikakken bayani akan waje da lokacin da Tinubu yayi maganar ba. 

Binciken mu bai nuna mana inda aka wallafa maganar ba a sahihan gidajen jarida. 

Tunde Rahman, maitaimakawa Tinubu akan kafafen yaɗa labarai, ya shaidawa Africa Check cewa ɗan siyasar bai yi wannan maganar ba. 

“A’a, bai ce haka ba,” Rahman ya shaidawa Africa Check. 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.