Back to Africa Check

Jiƙon ganyen itacen yalo baya ‘wanke’ ƙoda- aje a ga likita

ATAƘAICE: Wani rubutu a Facebook da ke yawo a Najeriya na iƙirarin cewa za’a iya amfani da ganyen yalo wanda aka fi sani da garden egg ko aubergine don ‘wanke’ ƙoda. Sai dai ƙwararru sun ce ba gaskiya ba ne.

A wani bidiyo da aka saka a Facebook a Najeriya, an nuna wata mace na magana da yaren Yarabanci da Turanci tana bayanin yadda za’a iya amfani da “ganyen yalo” don “wanke” ƙoda. 

Matar ta umarci masu kallo da su wanke ganyen kafin su tafasa don jiƙawa. Matar da ke cikin bidiyon ta ce za’a sha jiƙon da safe kafin karin kumallo. 

Yalo nau’i ne na itacen eggplant ko aubergine. Yana kuma daga cikin iyalan itacen nightshade, ana kuma cin sa a ko’ina a faɗin duniya. 

An kalli bidiyon sama da sau 100. Mun samu makamanciyar da’awar a nan, wadda ita kuma aka kalla sama da sau 68,000, duk da cewa shi wannan bidiyon umartar masu kallo yayi da su markaɗa ganyen yalon sannan a matse ruwan. 

An samu da’awar a nan, nan, nan, nan da nan

Shin za’a iya amfani da ganyen yalo don ‘tsaftace’ ƙoda? Mun duba. 

Kidneycleanse_false

Al’marar tsaftace ƙoda 

Tsaftace ƙoda na nufin sha ko cin wani abinci, ruwan wani abu da ƴaƴan itatuwa don “wanke” ƙoda. 

A cewar wasu likitoci mazauna Amurka da suka ƙware akan cutukan da suka shafi ƙoda na ƙungiyar Commonwealth Nephrology Associate, ƙoda bata ɓukatar wata tsaftacewa ta musamman. 

“Kasancewa cikin tsarin cin abinci mai gina jiki, mara gishiri da yawa, shan isasshen ruwa kullum, su ne kaɗai hanyoyin da ke sa ƙoda ta zama cikin ƙoshin lafiya,” ƙungiyar ta ce. 

Shafin yanar gizo mai bada bayanan kiwon lafiya na Healthline ya ce, matuƙar babu wata cuta a jikin mutum, ƙoda zata yi aikinta dai-dai ta hanyar cin abinci mai kyau da shan ruwa yadda ya kamata. 

Babu hujja a kimiyance da ta tabbatar da da’awar, a cewar ƙwararru

Africa Check ta tuntuɓi Fatiu Arogundade, likitan kula da ƙoda na asibitin koyarwa na jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ife, a kudu masu yammacin Najeriya, akan da’awar ta ganyen yalon. 

“Ba za’a iya amfani da shi ba don tsaftace ƙoda, kamar yadda suke iƙirari,” Arogundade ya ce. 

Ya ce duk da cewa ganyen yalo na tattare da tarin sinadaran bitamin, wanda zai iya kasancewa yana da antioksidan, ya ce amma ba zasu shafi aikin ƙoda ba ta kowacce siga. 

Ya bawa jama’a shawarar su ci abinci mai kyau da shan ruwa isasshe. 

“Idan kuna da cutar hawan jini ko siga, ku sha magungunan ku yadda ya dace,” Arogundade ya ce. 

Babaniji Omosule, likitan ƙoda a asibitin Worcestershire da ke Birtaniya, ya amince da hakan shi ma. Inda ya ce “Ba shi da wata hujja a kimiyance da ta goyi bayan da’awar”. 

Africa Check ta tantance da’awa da dama akan magungunan gida da ake iƙirarin suna tsaftace ko magani ga ƙoda. Ƙwararru sun ce babu wata hujja a likitance da ta goyi bayan waɗannan da’awowin. 


 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.