Back to Africa Check

Kar kuyi maganin matsalar tairod da hadin itatuwa

Wani saƙo da ke yawo a Facebook a Najeriya na cewa “maganin gida” na taimakawa wajen maganin tairod, maganin “warin baki, kwayoyin cuta a huhu da kumburin wuya (maƙoƙo).”

Saƙon ya bada shawarar haɗa magunguna daga” Aidan”, shuɗin ƙaro, ƴaƴan lara da zuma, a “sha rabin kofi kullum kafin a ci abinci.”

Tetrapleura tetraptera wanda Yarabawa ke kira da “aidan”, ɗan itace ne da ya samo asali daga yankin Afrika mafi zafi, an kuma yadda itacen na da amfani da kuma magani a jiki.

“Lara” na nufin itacen man kasto a harshen Yarabanci, wanda ake noma shi don haɗa magunguna a kuma sayar.

Shin wannan haɗin magunguna na magance matsalar tairod? Mun bincika.

Goitre_false

Maƙoƙo shine kumburin tairod

Sashen jiki da akafi sani da tairod gilan ana samun sa a gaban wuya. Shine kuma ke samar da sinadarin halitta na homons wanda ke da matuƙar muhimmanci wajen yin wasu ayyuka a jiki. 

Shi kuwa maƙoƙo kumburin tairod ne wanda ba na al’ada ba, wanda baya ciwo. Ba lalle ne ya shafi aikin tairod ba, ko ya jawo yawa ko raguwar sinadarin tairod ba.

Abubuwan da ke jawo maƙoƙo sun haɗa da kumburin tairod, ko tairod ɗin ya ringa aikin da ya gaza ko ya wuce ƙa’ida, sauyin sinadarin halitta wato homos, sankarar tairod, da kuma rashin sinadarin ayodin a abinci. Ana da masu fama da maƙoƙo kaɗan a ƙasashen da ake saka sinadarin ayodin a gishirin da ake amfani da shi.

Ƙaramin maƙoƙo ba ya ciwo, amma idan yayi tsanani  ya na iya jawo tari, wahalar haɗiyar abu da wahala wajen yin numfashi. 

Ana maganin sa da magunguna ko ayi aiki

Aihanuwa Eregie, Farfesa a fanin magungunan da cututtukan da suka shafi sinadaran jiki da tsokokin ƴaƴan halitta na jami’ar Benin a kudu masu yammacin Najeriya, ta shaidawa Africa Check bata yadda ayi maganin tairod da haɗin itatuwa ba.

“Maƙoƙo kawai kumburin sashen jiki da aka fi sani da tairod ne, kuma ana maganinsa bayan anyi la’akari da yanayin sa. Ta hanyar bada magani ko yin aiki,” ta ƙara da cewa.

Idan maƙoƙo yaƙi jin magani, sannan yana jawo wahala wajen numfashi ko haɗiya, hukumar kiwon lafiya ta Biritaniya tace sai ayi aiki don cire shi ko wani sashe na tairod ɗin.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.