Back to Africa Check

Ƙasar Sin bata gina ofishin ƴan sanda a Najeriya ba, kuma bata karɓi ragamar ayyukan hukumar hana fasa ƙauri ba

A taƙaice: Muhawara akan bashin da ƙasar Sin ke bin Najeriya na ta cigaba. Amma da’awar da ake cewa wannan babbar ƙasa ta yankin Asia na gina ofishin ƴan sanda a ƙasar da tafi kowacce ƙasa shahara a Afrika, har ma aka ƙara da cewa sun ɗau ragamar ayyukan hukumar fasa ƙauri ta Najeriya, bata da madogara.

 

“Ƴan’uwana ƴan Najeriya, shin kun san cewa tuni ƙasar Sin na gina ofishin ƴan sanda a Najeriya, sannan ƙasar Sin ta karɓi ragamar hukumar hana fasa ƙauri ta Najeriya? An nemar mana bauta ta dalilin bashi kenan.”

Wannan shine saƙon da ake ta kwafa ana mannawa a wurare daban-daban a Facebook a watan Oktoban 2022. 

“Najeriya kwastam” na nufin hukumar hana fasa ƙauri ta Najeriya.

Alaƙar diflomasiya tsakanin Najeriya da ƙasar Sin ta samo asali tun shekarar 1971. 

Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaryata da’awar da ke cewa bashin ƙasar Sin ga Najeriya wani tarko ne. Sai dai jama’a na cigaba da muhawara akan basussuka da ƙasar Sin ke bin Najeriya

Gwamnatin ƙasar Sin ta gina ofishin ƴan sanda a Najeriya, kuma ta ɗau ragamar kula da fasa ƙauri? Mun bincika. 

ChinaNigeria_False_0.png

Da’awar bata da wata hujja

Babu ɗaya daga cikin sakonnin na Facebook da ya bayyana yadda da kuma inda aka samo labarin. Wannan rashin bayanai na nuna cewa da’awar ta ƙarya ce.

Babu wani babban gidan jarida a gida da waje da ya ruwaito cewa ƙasar Sin na gina ofishin ƴan sanda ko karɓar ragamar kula da fasa ƙauri a ƙasar. Idan da gaskiya ne, da ya zama kanun labarai. 

Gidajen jarida na gida sun ruwaito cewa gwamnatin ƙasar Sin ta musanta da’awar cewa tana gina ofishin ƴan sanda a Najeriya. 

Binciken shafin gwamnatin ƙasar Sin na yanar gizo bai bamu wata hujjar da zata tabbatar da da’awar ba.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.