Back to Africa Check

A kiyayi ƴan damfara - waɗannan hanyoyin saka hannun jari basu samu amincewar babban bankin Najeriya ba

A TAƘAICE: Wani shirin saka hannun jari na bogi, wanda aka bayyana shi a matsayin yaudara tun a watan Nuwanban 2022, ya sake bayyana a yanar gizo da makamantan hanyoyin da suka yi amfani da su a baya. Damfara ce, don haka ku kiyaye kuɗaɗen ku. 

 

Wani rubutu da aka rarraba a wani shafin Facebook mai suna Nigeria CBN investment trading platform, ya ce babban bankin Najeriya CBN ya amince ko yana da wuraren saka hannun jari guda biyu. 

Rubutun ya bayyana su a matsayin “wajen saka hannun jari na helping hands investment trading platform” da kuma “wajen cinkayya na lovecaincryptocurrency”. 

Saboda wurin ya samu albarka da goyan bayan babban banki, masu amfani da shi zasu iya saka hannun jari cikin kwanciyar hankali, rubutun ya ce. Ya kuma buƙaci waɗanda su ke so da su tuntuɓi Mr Musa Solomon, wanda suka bada lambar wayarsa. 

Rubutun na haɗe da hoton abun da yayi kama da shaidar aiki ta wani Solomon, wadda ake zaton kamar babban bankin Najeriya (CBN) ne ya bayar. 

Rubutun ya bayar da liyink da dama na WhatsApp ga waɗanda suke buƙata da su tura saƙo ta wajen. 

Mun samu makamancin saƙon da ke tallata shirin saka hannun jari amma da bambancin suna da lamba a nan, nan, nan, nan da nan

Shin shirin saka hannun jarin na gaskiya ne? Mun bincika. 

CBN_Scam.

CBN ta nesanta kanta daga shirin hannayen jari na bogi

Mun buɗe ɗaya daga cikin link na WhatsApp da ke tare da rubutun, muka kuma yi kamar muna da ra’ayi, mun samu damar zantawa da wani da ake kira Solomon. Ya bamu takardar yin rijista da ke ɗauke da tambarin CBN a jiki. 

Sannan aka aiko da dogon saƙo da ke bayyana adadin kuɗi a kuɗin Najeriya da za’a iya saka hannun jari da su a cikin shirin da kuma abun da za’a samu bayan an saka hannun jarin. 

Sai dai kuma da muka buƙaci da a bamu link na shirin daga shafin CBN na yanar gizo, sai aka daina amsa mana. 

Wani link kuma da aka gabatar a rubutun ya buƙaci da mu shiga wani guruf a WhatsApp mai mutane sama da 332, wanda ganin hakan ya nuna mana cewa wasu sun faɗa cikin tarkon masu damfarar. 

Shirin saka hannun jarin ba daga babban banki ya ke ba, mai magana da yawun babban bankin Isa Abdulmumin ya shaidawa Africa Check. Katin shaidar aikin ma na “bogi” ne, a cewar sa. 

A watan Nuwamba 2022, Africa Check ta samu cewa wajen saka hannun jari na “helping hands investment trading platform” na bogi ne. Haka nan bayan shekara guda ma ta tabbata na bogi ne, tare da wajen saka hannun jarin cinikayya na “lovecaincryptocurrency” da wasu wuraren saka hannun jari da dama. 

Ku kiyaye kuɗaɗen ku, ku karanta hanyoyin da zaku gano wuraren saka hannun jari masu hatsari a Facebook a nan

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.