Wani saƙo da ke yawo a WhatsApp a Najeriya na iƙirarin cewa koka- kola na bada kyautar kuɗi don bikin murnar cikar kamfanin shekaru 135 da buɗewa.
Saƙon wanda ba’a rubuta shi da kyau ba, ya na cewa: “ Bikin cikar Koka- Kola shekaru 135! Za ku ci 416464₦ kyauta. Na samu nawa.”
Saƙon ya haɗa da wajen da za’a latsa a faɗa wani shafi da ba’a tsara shi da kyau ba, inda ake buƙatar mutane su amsa tambayoyi guda uku.
Hakan dai zai yi wuya, shin gaskiya ne Koka- Kola na bada kyauta?
Ku kiyaye bayanan kan ku
Koka- Kola tayi bikin cikarta shekaru 135 a watan Mayun 2021. Rubutu irin wannan za’a same shi ne a shafukan kamfanin Koka- Kola Najeriya na Instagram da Twitter.
Ba mu samu wani saƙo makamancin wannan ko na wata gasa ba daga shafin Koka- Kola ko shafukan kamfanin na sada zumunta ba.
Zai yi wuya a ce kamfani mamallakin biliyoyin daloli a faɗin duniya zai bada wata garaɓasa a shafin yanar gizon da ba mallakarsa ba ko ta saƙon WhatsApp.
Africa Check ta taɓa tantance da’awa makamanciyar wannan da ke amfani da manyan sanannun sunayen wajen samun bayanan jama’a na sirri. Domin samun karin bayani a karanta rubutun mu akan hanyoyin gano damfara a Facebook.
For publishers: what to do if your post is rated false
A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?
Click on our guide for the steps you should follow.
Publishers guideAfrica Check teams up with Facebook
Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.
The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.
You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.
Add new comment