Back to Africa Check

Ruwan ganyen gwaza baya maganin basir

Wani saƙo da ke yawo a Facebook na iƙirarin cewa “ƙarfin magani” da “ruwan” tsirrai zai yi maganin basir. 

Ƙasan taken na cewa “kuyi maganin basir”: “Kuyi amfani da ƙarfin maganin da ke cikin wannan ruwan gwazan da zan sanar da ku. Ruwan yana aiki ga basir, wanda aka fi sani da Ako Jedi (da Yarabanci).”

Gwaza ko taro, amfanin gona ne da ake ci, ya ke kuma fitowa daga saiwarsa, sai dai ana iya cin ilahirin ɗan itacen. 

Rubutun na Facebook ya bayyana yadda za’a yanka ganyen gwaza a saka a basir ɗin, sannan rubutun ya ce “ruwan zai saka basir ɗin komawa. An gwada an kuma amince”. 

Ruwan gwaza zai yi maganin basir? Mun bincika. 

Cocoyam_False

Sanin dalilin ciwo ne zai sa asan irin maganin da za’a yi 

 

Basir, kumburin jijiyoyin ƙasan dubura ne da kuma kewayen duburar, wanda zai iya kasancewa a ciki ko daga waje

Alamun ciwon sun haɗa da ciwo ko rashin jin daɗi a wajen, kumburi, fitar jini da fitowar basir ɗin daga dubura. 

Mun tambayi Dr Joanah Ikobah, wadda babbar likitar yara ce da ta ƙware akan cututtukan cikin ciki da cututtukan hanta, kuma babbar malama a jami’ar Calabar a Kudancin Najeriya, akan wannan magani ta hanyar amfani da gwaza. 

“Ruwan gwaza ba maganin basir ba ne. Da farko ya kamata a san abun da ya ke jawo basir ɗin, kamar a tabbata mara lafiya bashi da matsalar wahalar fitar bayan gida ko taurin bayan gida. [Wannan matsalar] ana iya maganin ta a asibiti, a wasu lokutan kuma sai anyi aiki,” likitar ta ce.

Ikobah ta ce mafi akasari, dalili da kuma tsananin ciwon ne zai bayyana yadda za’ayi maganin ciwon. 

A cewar hukumar lafiya ta Biritaniya, za’a iya maganin basir ko a kiyaye kamuwa da shi ta hanyar shan ruwa mai yawa, cin abinci mai ɗauke da sinadarin faiba, yin wanka da ruwan ɗumi don rage raɗaɗin ciwon ko ƙaiƙayi, motsa jiki akai-akai da kuma rage shan barasa ko abincin da ke ɗauke da sinadarin kaffain a ciki. 

A duba da’awar da Africa Check ta ƙaryata a baya da ke magana akan haɗin da akeyi don maganin basir

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.