Back to Africa Check

Sam, ana buƙatar ma’aikatan kamfanin yin allurar rigakafi da ma’aikatan gwamnatin Amurka da su yi allurar rigakafin Covid-19

“Jerin ma’aikatan da BA’A buƙatar suyi allurar rigakafi,” farkon abun da wani rubutu da ke kan wani hoto da aka yaɗa sama da sau 13,000 a Facebook a Afrika ta Kudu ya ƙunsa. 

White House, fadar shugaban ƙasar Amurka, na cikin manya hukumomi guda bakwai da aka lissafa. Sannan aka lissafo wasu manyan cibiyoyin kiwon lafiya guda uku: Hukumar kula da cututtaka masu yaɗuwa ta Amurka (CDC) da kuma hukumar kula da abinci da magunguna (FDA) da kuma Hukumar lafiya ta Duniya wato WHO.

An kuma ambaci kwanfanoni guda uku da suka yi alluran rigakafin Covid-19, wato Pfizer, Moderna da Johnson & Johnson

“interesting, veral in die lig daarvan dat sekere SA maatskapye al reeds die jab verpligtend will maak, nog voor dit wet is…!?” abun da rubutun da ke jikin hoton ke cewa. Wannan na nufin : “Abun sha’awa, musamman kasancewar wasu kamfanoni a Afrika ta Kudu na son wajabta allurar riga, tun kafin hakan ma ya zama doka…!?”

A watan Junin 2021, ministan ƙwadago na Afrika ta Kudu Thulas Nxesi ya gabatar da wani “bincike a matakai uku” waɗanda ma’aikatu zasu bi don zamar da allurar wajibi ga ma’aikatan su.

Bayan wata guda kuma, a 18 ga watan Agusta, cibiyar makarantu ta Curro mai zaman kanta ta bayyana cewa zata yiwa duka ma’aikatanta allurar rigakafin kafin ƙarshen shekarar 2021.

 Haka nan a wani yunƙuri da aka ƙwatanta a matsayin na nuna “ƙarfin hali”, babban kamfanin inshora na ƙasar Discovery ya bi sahu wajen cewa zai fara neman ganin cewa duka ma’aikatan su sunyi allurar a farkon shekarar 2022.

Anata cigaba da muhawara akan ko allurar rigakafi ga ma’akata zata zama biyayya ko doka. Amma ƙasashe da dama sun mai da allurar dole, musamman ga ma’aikatan kiwon lafiya da kuma waɗanda ke cikin tsananin hatsarin kamuwa da cutar.

Da gaske ba’a buƙatar ma’aikatan waɗannan hukumomi guda bakwai da aka lissafa a hoton suyi allurar rigakafi? Mun bincika.

employer_partly_false

Ma’akatan gwamnatin Amurka dole ne suyi allurar rigakafi 

A lokacin da aka rarraba rubutun a Afrika ta Kudu, a ranar 2 ga watan Satumba 2021, yin allurar rigakafi bai zama wajibi ga ma’aikatan gwamnatin Amurka ba. Wannan ya haɗa da fadar shugaban ƙasa, CDC da kuma FDA- duk hukumomin gwamnati.

A ranar 29 ga watan Juli, shugaban ƙasar Amurka Joe Biden yace duk ma’aikata da ƴan kwangila dole ne su “tabbata sunyi ko basuyi allurar rigakafin ba.”

Inda aka buƙaci waɗanda basu yi allurar ba da su saka takunkumin rufe fuska a duk lokacin da suke aiki, su yi gwaji sau ɗaya ko biyu a sati, su bada tazara kuma baza’a bari suyi wata tafiya da ta danganci aiki ba.

Amma a ranar 9 ga watan Satumba Biden ya rattaba hannu akan dokokin da za’a zartar guda biyu waɗanda ke tilastawa ma’aikata da masu aikin ƙwangila na gwamnati yin allurar rigakafin.

“Mun yi hakuri, amma hakurin mu na raguwa, kuma ƙin amincewar ku ya jawo mana,” Biden yace a wata sanarwa da yayi a gidajen talabijin.

Biden tuni yayi cikakkiyar allurar rigakafi.

Ba’a buƙatar ma’aikatan hukumar lafiya ta duniya da suyi allurar rigakfi 

Ma’aikatan WHO ba sai sunyi allurar rigakafin ba. A wata taƙaitacciyar shawara da aka yanke, wadda aka raba a watan Afrilu 2021, hukumar ta ce ita dai bata ce ta yarda ko ta ƙi yarda ta sa ma’aikatanta lalle suyi allurar rigakafin ba.

“Masu bada shawara na gwamnatoci da hukumomi ya kamata suyi amfani da salon muhawara don bawa ma’aikata ƙwarin gwiwar zuwa suyi allurar don karan kansu kafin yin allurar ya zama doka,” cewar shawarar. 

“Za’a iya saka matakai masu tsauri ne matuƙar wannan hanyar bata yi tasiri ba.”

Kamfanonin yin alluran rigakafi sun wajabtawa ma’aikatan su yin allurar rigakafin

A wata sanarwa daga hukumar watsa labarai ta Amurka CNBC, Pfizer sun ce ma’aikatan su ƴan asalin ƙasar Amurka da masu aikin ƙwangila wajibi ne suyi allurar rigakafin ko su ringa yin gwajin cutar duk sati. Kamfanin ya ƙara da bawa bangarorin kamfanin da ke wasu ƙasashe shawarar da su bi wannan dokar.

Moderna ta tilastwa ma’aikatan ta da ke Amurka da su yi allurar kafin ranar 1 ga watan Oktoba 2021, a wata sanarwa da kamfanin ya fitar.

Kamfanin watsa labarai mallakar Amurka, USA Today, ya tantance labari makamancin wannan, wanda aka rarraba a kafafen sada zumunta a Amurkan. Mai magana da yawun kamfanin Johnson & Johnson Lisa Cannellos ta shaida musu cewa duka ma’akatansu dole ya zamana sun karɓi cikakkiyar allurar rigakafi kafin 4 ga watan Oktoba.

Amma duka waɗannan kamfanoni sunce zasu karɓi uzurin ma’aikatan da wasu dalilai na addini ko lafiya suka hana su yin allurar.

Alluran rigakafi na Pfizer-BioNTech da Johnson & Johnson duka hukumar kula da kayan kiwon lafiya ta Afrika ta Kudu ko Sahpra ta amince da su. Hukumar bata karɓi wata takardar neman izini daga kamfanin Moderna ba.

AstraZeneca kuma fa, ta samu amincewa a Afrika ta Kudu?

Sahpra ta amince da allurar rigakafi ta Oxford- AstraZeneca.

Da farko gwamnati ta yanke shawarar kar tayi amfani da allurar AstraZeneca saboda rashin ƙarfinta wajen yaƙi da nau’in Covid-19 na Beta, lokacin da yake ta yaɗuwa a ƙasar.

A ranar 30 ga watan Juli mataimakin ministan lafiya Joe Phaala ya ce suna duba yiwuwar sake yin sabon bincike akan ingancin allurar wajen yaƙar nau’in cutar na Delta. Amma har yanzu ba’a fara amfani da allurar rigakafin a Afrika ta Kudu ba.

Mun bincika saboda gaba, mun samu cewa ma’aikatan AstraZeneca da ke Amurka ana buƙatar suyi allurar rigakafin.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.