Back to Africa Check

Shin jama’a a Najeriya zasu iya buɗe katin layin waya ba tare da lambar shaidar ɗan ƙasa ba? Ba haka ba ne saƙon zamba ce

“Idan katin layin wayar ku na cikin katuna miliyan 75 da NCC ta haramta amfani da su kuna daf da a ɗage haramtawar da aka yiwa layin ku, kuma a kyauta, abun da wani saƙo dake yawo a Facebook Najeriya tun watan Afrilun 2022 ke cewa.

NCC itace hukumar sadarwa ta Najeriya, hukumar da ke da alhakin kula da sadarwa ta ƙasa. 

Saƙon na iƙirarin cewa masu amfani da wayar hannun da aka toshewa layukan su, zasu iya buɗe layukan ta hanyar bin wannan mahaɗar da aka bayar. 

“Kuyi sauri ku buɗe na ku, yanzun nan na buɗe LAYUKA na guda uku a kyauta. Kar ku zama marowata, ku rarraba wannan da abokai da kuma guruf, saƙon ya ƙara da cewa.

A watan Afrilu, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da bawa kamfanun nukan sadarwa damar toshe duk layin wayar da ba’a haɗa shi da lambar shaidar ɗan ƙasa ba (NIN). 

An ƙiyasta cewa layukan waya miliyan 72 aka toshe, hakan ya sa masu layukan kasa amfani da wayoyinsu. 

Amma za’a iya buɗe wayoyi idan akayi amfani da mahaɗar da ke tare da wannan saƙo? Mun bincika. 

Simcard_Scam

NCC: Ayi watsi da saƙo mai ɗauke da ‘ɓarna’

A ranar 11 ga watan Afrilu, NCC ta fitar da sanarwar ga ƴan jarida da ke gargaɗi akan wannan saƙon.

“Mahaɗar da zata kai mutum wani shafi da kuma abubawan da aka ambata a saƙon na nuna bayanan da ba’a fahimta ba da bayanan ƙarya, waɗanda aka tsara don su yaudari jama’a akan layukan wayar da aka hana kira da su saboda gazawarsu wajen haɗa layukan da NIN har ƙarshen wa’adin da aka ƙayyade,” a cewar sanarwar. 

“Saƙon mai ɓatarwa, ya nuna tambarin hukumar NCC, ya kuma yiwa mutane alƙawarin cewa da sun latsa mahaɗar suka kuma bi umarnin da aka bayar, masu amfani da layukan kowanne kamfanin sadarwa, waɗanda aka toshewa layukan zasu iya buɗe layukan ba tare da lambar NIN ba.”

Sanarwa ta ƙara da cewa saƙon da kuma yaɗawar ba daga hukumar NCC ya fito ba, kuma hukumar bata ce masu layukan waya zasu iya buɗe layukan su ba tare da lambar NIN ba. 

“Don haka, ayi watsi da wannan saƙo.”

Zamba ta amfani da saƙon imel

Mahaɗar da ke cikin saƙon na kai mutum wani shafin bulog da ke neman masu ziyara da su saka lambobin wayoyinsu don samun kuɗin kiran waya da datar shiga yanar gizo a kyauta. 

Adireshin URLs da kuskuren rubuta kalmomi na nuna cewa zamba ta amfani da imel - a yanar gizo ce da ke cewa daga ingantaccen tushe ta fito, ta kuma tambayi jama’a su bada bayanan kan su. Wannan zai iya sawa a saci bayanan ku ayi amfani da su. 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.