Back to Africa Check

Tsohon shugaban ƙasa Obasanjo bai tsayar da Tinubu, ɗan takara daga jam’iyya mai mulki a matsayin ɗan takarar sa na shugaban ƙasa ba

A TAƘAICE: A wasu saƙonni da aka wallafa a kafafen sada zumunta a Najeriya, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya nuna kamar ya tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar APC- Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar sa na shugaban ƙasa. Maganganun ƙirƙirar su akayi kuma tsayar da shi da ake cewa yayi, ƙarya ce.

Wani hoton allon waya wato sikirinshot da ke yawo a Facebook Najeriya na ɗauke da wasu maganganu da suka bayyana cewa daga bakin tsohon wanda yayi shugabancin ƙasar nan har sau biyu Olusegun Obasanjo suka fito, suna cewa ya tsayar da Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa mai jiran gado.

Tinubu tsohon gwamnan jihar Legas ne, wadda ke kudu maso yammacin Najeriya, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyya mai mulki All Progressive Congress

Rubutun jikin hoton allon wayar wanda ke haɗe da hoton Obasanjo da Tinubu, ya na cewa; “Ni ba ɗan siyasa ba ne, ni soja ne da aka karrama kuma mai muƙamin janar na sojojin ƙasa. Idan kuna neman cikakken ɗan siyasa, na ajin farko ku je Bourdillon da Legas, a nan zaku same shi.”

Tinubu na zaune a titin Bourdillon da ke unguwar Ikoyi a Legas, wanda rukunin gidaje ne na masu faɗa aji.

Bayan a bayyane sun yi iƙirarin cewa wai “ya kusa hallaka gwamnatin Tinubu da jiharsa”, an kuma ruwaito Obasanjon na cewa wai Tinubu “ya tsallake ne saboda yana da wani ƙarfi na daban. Mu na fatan zai samu damar nuna wannan ƙarfi a Najeriya”.

Obasanjo yayi shugaban Najeriya a lokacin mulkin soja tsakanin shekarun 1976 zuwa 1979, sannan yayi shugaban ƙasa a matsayin farar hula a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar People’s Democratic Party.

Hoton allon wayar da aka buga a ranar 7 ga watan Oktoba 2022, an sake wallafa shi a nan da nan

Amma Obasanjo ya bayyana Tinubu a matsayin “cikakken ɗan siyasa’’ kuma mai wani “ƙarfin iko”

Obasanjo_False 2_0

Obasanjo: Wannan “ƙarya ce kuma bogi”

Obasanjo ya musanta cewa ya tsayar da Tinubu a wata sanarwa da mataimakinsa akan yaɗa labarai Kehinde Akinyemi ya fitar. 

A wata sanarwa da Africa Check ta samu, Obasanjo ya ce: “Rundunar Soja ce kawai take horar da jami’anta su zama masu iya juya jama’a da abubuwa. Don haka, ba zan ci mutuncin aikina na siyasa ba wanda baya buƙatar wani horo na musamman. Wannan ƙarya ce kuma bogi”. 

Manyan wuraren yaɗa labarai da dama sun wallafa wannan sanarwar suna jayayyar tsayarwar da aka ce Obasanjo ya yiwa Tinubu. Ƙarya ce. 


 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.