Back to Africa Check

Wa’adin lambar tantancewa ta Banki a Najeriya ba zai ƙare bayan shekaru 10 ba

Wani bidiyon TikTok da ke yawo a kafar sada zumunta ta Facebook Najeriya na iƙirarin cewa lambar tantancewa ta banki (BVN) da babban bankin Najeriya (CBN) ya ƙirƙira ƙarshen wa’adin ta zai yi bayan shekaru 10. 

A shekarar 2014, babban banki tare da duk bankunan Najeriya suka ƙirƙiri tsarin gano masu ajiya a banki na bai ɗaya. 

An ƙirƙiri lambar tantancewar mai lambobi guda 11 don kare mu’amullar cinikayya a bankuna daga ƴan damfara, hanyar sanin kwastomomi da kuma hanyar tantance su waye kwastomominsu. 

Rubutun da ke tare da bidiyon na TikTok na cewa: “Wa’adin BVN ɗin ku zai ƙare.”

Bidiyon na tsahon awa guda da mintuna 57, ya na nuna wani mutum da ba’a san ko waye ba yana magana, yana cewa zai bayyana ɗaya daga cikin manyan sirrukan bankuna a Najeriya.”

Bidiyon na tare da wani hoton allon waya wato sikirinshot na wani shafin yanar gizo, wanda mutumin yayi iƙirarin yana ɗauke da bayanan da ke bayyana lokacin ƙarshen wa’adin BVN, wanda ya ce shekaru 10 ne. 

An rarraba bidiyon a Facebook a nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan, nan da nan

Wannan wa’adi idan gaskiya ne, zai kasance a shekarar 2024, wato shekaru 10 bayan fara ƙaddamar da shi. Wannan zai tilastawa ƴan Najeriya har waɗanda ke ƙasashen ƙetare sake sabunta lambar. 

Shin da’awar da ke cikin bidiyon gaskiya ce?

BVN_False

Babban banki ya ce wa’adin BVN baya ƙarewa

Wasu masu tantance labarai sun ce an bayyana wannan wa’adin a wani rubutu da aka buga aka kuma cire a shafin babban bankin na yanar gizo. 

A Mayu 2023, CBN ta wallafa a shafinta na Tiwita cewa BVN da ake bayarwa a Najeriya ba shi da wa’adin ƙarewa: “Da zarar na’urar tattara bayanan mutum ta tattara bayanai ta kuma shigar da su cikin kundin bayanai na hukumar kula da bankuna ta Najeriya (NIBSS), BVN ta zauna kenan har abada.”

Wannan da’awar ta ƙarya ce, kuma zata iya sa miliyoyin ƴan Najeriya yin tururuwa zuwa bankunan su a shekarar 2024 don ƙokarin sake sabunta BVN ɗin su.

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.