Back to Africa Check

Wannan haɗin ba zai ‘tsaftace’ mahaifa ba- a tuntuɓi likitoci

ATAƘAICE: Wani rubutu a Facebook na iƙirarin cewa wani haɗi da aka bada shawarar a yi yana ‘tsaftace’ mahaifa. Ƙwararru sun ce babu hujjar da ta tabbatar da hakan

 

“Wannan haɗin na taimakawa wajen wanke mahaifa da kuma buɗe bututun mahaifa wanda shi ke jawo rashin haihuwa,” wani rubutu na Facebook ke cewa. 

Rubutun wanda aka yi shi a ranar 7 ga watan Yuni 2023, ya bayyana abubuwan da za’a tanada don haɗin: Lemon tsami, borkonon negro, aidan, citta da kanunfari. 

Sannan aka faɗawa masu karatu yadda zasu haɗa haɗin da yadda za’a sha. 

“A gyara, a yanka kayan haɗin, a tafasa su na tsahon mintuna 40, sai a bar shi ya huce kafin a sha. Kar a ƙara ruwa da yawa, a saka dai-dai misali. A sha ƙaramin kofi safe da yamma, na tsahon sati guda,” rubutun ke cewa.

A cewar rubutun haɗin ya “haramta ga mata masu cutar gyambon ciki” amma maza zasu iya sha bayan sun ƙara tsamiya a ciki. 

An rarraba rubutun sau da dama, har an samu tsokacin da ke godewa wanda yayi rubutun. Mun kuma samu irin da’awar a nan

Da gaske ne haɗin na “tsaftace” mahaifa, yayi kuma maganin rashin haihuwa? Mun yi wa da’awar duba a tsanake. 

Uteruscleanse_false

Menene tsaftace mahaifa

Mahaifa wani sashe ne mai muhimmanci a jikin mace. Shi ne wajen da jarirai ke girma kafin haihuwarsu. Matsala a mahaifar ka iya shafar haihuwa

A wasu lokuta ana yin wankin mahaifar da aka fi sani da (D&C) don cire tsoka daga cikin mahaifa ko a “wanke” mahaifar, a cewar Mayo clinic wata ƙungiya mai zamankanta. Wani lokacin ana haɗa D&C da cire mahaifa ta hanyar saka wata na’ura ƙarama mai haske da kemara a cikin mahaifar. 

Ana amfani da waɗannan hanyoyi wajen cire tsoka, ƙari, mabiya bayan an haihu da kuma fitowar wani abu a bakin mahaifa. 

Masana sun ce ‘wanke’ mahaifa ‘bashi da wata hujja a kimiyance’

Waɗannan da’awowi basu da wata hujja a kimiyance. A halin yanzu babu wani abu “wanke mahaifa,” Oladapo Olayemi, Farfesa a bangaren lalurar mata da kuma kula da lafiyar mata masu juna biyu a jami’ar Ibadan, ya shaidawa Africa Check. 

Farfesan ya ce babu wani bincike da akayi da zai tabbatar da abun da aka ambata a game da wannan haɗi. 

“Babu wani dalili a kimiyance da zai sa a yi hasashen yin gwajin yin bincike akan lamarin. Waɗannan abubuwa ana amfani da su ne don ci, kuma babu wani abu da ya nuna cewa bayan cin su, suna da wani tasiri a mahaifa, koda ga dabbobi ne,” ya ce. 

Ya bada shawara ga masu lalurar rashin haihuwa da su je suga ƙwararrun likitoci don samun shawarwarin da su ka dace. 

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.