Back to Africa Check

Haɗin albasa, shuwaka da zuma ba zasu magance cutar sikari nau’i na 1 da na 2 ba

Wani saƙo da ke ta yawo a shafukan Facebook a Najeriya na cewa wai haɗin albasa, shuwaka da zuma zai magance cutar sikari nau’i na 1 da na 2.

Saƙon ya bada umarnin a markaɗa’ albasa guda 6’, sannan a haɗa da’ ganyen shuwaka cikin tafin hannu’ ko wani itace da ake kira vernonia amygdania, sannan a saka zuma a cikin haɗin.

Saƙon ya ce a sha babban cokali biyu na haɗin safe, rana da dare tsahon makwanni biyu, tabbas za’a ‘warke sarai’ daga cutar.

Ciwon suga nau’i na 1 na afkuwa ne lokacin da aka ce fankiriyas na cikin mutum ya gaza samar da isasshan sinadarin insulin a jikin mutum. Sinadarin insulin shine sinadarin da jikin mutum ke amfani da shi wajen amfani da sikari ko maikon da ke shiga jiki.

Ciwon suga nau’i na 2 wanda aka fi sani da rashin amsar insulin, na afkuwa ne lokacin da jiki ya ƙi karɓar insulin din da fankiriyas ke fitarwa ko ya ƙi amfani da shi yadda ya kamata.

Shin wannan haɗin na gida zai magance cutar sikari?

 

prof_false

 

Cutar sikari bata da magani- amma ana iya rayuwa da ita

A cewar hukumar kiyayye cututta ta Amurka, ciwon sikari nau’i na 2 yafi kama mutane yan shekaru 45 zuwa sama, amma ana samun ƙananan yara da matasa da ka iya kamuwa da cutar.

Daga cikin abubuwan da ke jawo barazanar kamuwa da cutar sun haɗa da samun cutar a cikin zuri’a, yawan shekaru, ƙwayoyin halitta, ƙiba da rashin motsa jiki a cewar hukumar lafiya ta duniya. 

Africa Check ta tuntuɓi wani farfesa akan magunguna da cututtakan na Jami’ar Benin Aihanuwa Eregie akan batun.

“ A wannan lokacin babu maganin ciwon sikari, a na dai kawai kula da masu cutar ne. Akwai daidaita abun da za’a ci wanda ya haɗa da cin abincin da ya dace sai kuma motsa jiki kamar yadda likitoci suka umarta. Akwai kuma magunguna kala kala da suka haɗa da ƙwayoyin magani da allurai, da za’a ringa amfani da su don dai daita yawan sikari a jiki, duk hakan ya danganta da nau’in ciwon da mutum ke ɗauke da shi,”  Eregie ya faɗa.

Eregie ya ce waɗannan maganganu da haɗe haɗe zasu iya sa marasa lafiyan da suka daina shan magani su ƙare a asibiti da wata matsalar matsananciya.

Africa Check ta taɓa tantance makamanciyar wannan da’awar. Kamar dai waɗancan da’awowin haɗin albasa, shuwaka da zuma basa maganin ciwon sikari nau’i na 1 da na 2. 

Gwajin jini ne kawai zai tabbatar da ko mutum na ɗauke da cutar da irin nau’in da ya ke ɗauke da shi, kuma masana sun bada shawarar yin gwajin sikari lokaci zuwa lokaci.

 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.