Back to Africa Check

Link ɗin da ke zagaya Facebook ba na ainihin wajen cike gurbin neman aikin rundunar ƴan sandan Najeriya ba ne

A TAƘAICE: Za’a rufe shirin ɗaukar ma’aikata na rundunar ƴan Najeriya a ranar 26 ga watan Nuwamban 2023. Amma dai link ɗin da takardar cike gurbin aikin da ke zagawa a Facebook ba na gaskiya ba ne. Waɗanda suke neman aikin zasu bi sahihin shafin rundunar na yanar gizo da kuma shafin rundunar na kafafen sada zumunta don samun cikakken bayanin yadda ake neman gurbin. 

 

“LINK NA CIKE GURBIN AIKI RUNDUNAR ƳAN SANDA. Link; (https://tinyurl.com/Apply-NigeriaPolice),” saƙon na Facebook ke cewa. 

Maƙale a jikin saƙon hoton abun da yayi kama da takardar neman aiki ce, wadda ke ɗauke da tambarin Najeriya

Mun gano makamantan ta a nan, nan, nan da nan. Duk da cewa ba’a samu waɗanda suka yi tsokaci a saƙon ba, wasu sun rarraba saƙon a guruf- guruf ɗin da ke ɗauke da dubban jama’a. 

Link ɗin da aka gabatar a saƙon na gaske ne? Mun bincika. 

NigeriaPoliceRecruitment_Scam


WURAREN CIKE GURBIN NEMAN AIKI NA BOGI NA IYA SATAR BAYANAN KU

Mun danna link ɗin, ya kuma kai mu wani shafin yanar gizo, wanda yayi kama da ba na gaskiya ba, wanda ya buƙaci da mu cike bayanan mu, kamar suna, jinsi da ƙasar da muke zaune. 

Bayan mun saka bayanan, sai aka kai mu wani shafin, wanda ke cewa: “Takardar neman AIKIN RUNDUNAR ƳAN SANDA. Ana dubata a halin yanzu. Ku tabbatar da sunan ku kafin ku kai mataki na gaba. Ku sani! An taƙaice yawan waɗanda zasu nema.”

Shafin ya nuna abun da yayi kama da saƙon Facebook, da ke da waɗanda suka so saƙon har sama da mutane 160, 000, yayin da sama da mutane 30, 000 suka rarraba, suka kuma yi tsokaci, waɗanda da dama suke iƙirarin cewa an amince da takardun nasu na neman aikin.

Shafi na uku kuma na takardar neman aikin na yi mana murna da kuma bamu umarnin mu raba link ɗin zuwa guruf guda biyar ko abokan mu na WhatsApp guda 15. Sai dai kuma, an ƙyale mu mun cigaba ba tare da mun rarraba link ɗin a WhatsApp ba, wanda hakan ya ƙara sa mu tantama akan abun. 

A shafi na ƙarshe an nuna mana wajen da ke cewa “a buga yanzu”, don mu buga takardar neman aikin. Da muka danna wajen, sai ya kai mu wani wajen da bashi da alaƙa da ɗaukar aiki a rundunar. 

Irin wannan shirin shi ake kira da dabarar samun masu shiga shafi ta hanyar yin ƙarya. Irin waɗannan shafuka na neman magoya baya da su yi tsokaci, su rarraba su kuma ƙaunaci saƙon. Yawan waɗanda sukayi hakan, shi zai ƙara tallata shafi da kuma ƙara yawan masu shiga shafi. Irin waɗannan suna saka saƙonni masu tada hankali ko na yaudara. 

‘A tantance sahihancin waje ko bayanan ɗaukar aiki,’ rundunar ƴan sanda ta gargaɗi jama’a

Mun binciki sahihin shafin rundunar ƴan sandan Najeriya na yanar gizo da shafin su na kafar sada zumunta ta Facebook, amma bamu samu bayanin takardar ɗaukar aiki ko link makamancin wanda aka saka a saƙon

A cewar shafin yanar gizo na gidan jaridar Punch, shirin ɗaukar aikin rundunar na yanar gizo an fara shi daga ranar 15 ga watan Oktoba zuwa 26 ga watan Nuwamba 2023. 

A watan Oktoba, rundunar ƴan sandan ta gargaɗi jama’a a shafin ta na X wanda aka fi sani da Twitter a da, akan a guji ire-iren waɗannan shafuka na ƴan damfara. 

“Muna matuƙar gargaɗin masu son neman aiki da su bi hanyoyin da ya dace su kuma tantance sahihanci duk wani waje da bayanin ɗaukar aiki kafin su aiwatar da komai. Kar masu damfara su yaudare ku. Kasancewar ku cikin aminci da tsaro shine abun da muka bawa muhimmanci,” rundunar ƴan sandan ta rubuta.  

Sun kuma buƙaci masu son neman aikin da su je wannan shafin yanar gizon policerecruitment.gov.ng don tura takardun neman aikin. 

Don ƙara kiyaye kanku daga masu damfara a yanar gizo, ku karanta waɗanda hanyoyin da muka jero a nan



 

Republish our content for free

We believe that everyone needs the facts.

You can republish the text of this article free of charge, both online and in print. However, we ask that you pay attention to these simple guidelines. In a nutshell:

1. Do not include images, as in most cases we do not own the copyright.

2. Please do not edit the article.

3. Make sure you credit "Africa Check" in the byline and don't forget to mention that the article was originally published on africacheck.org.

For publishers: what to do if your post is rated false

A fact-checker has rated your Facebook or Instagram post as “false”, “altered”, “partly false” or “missing context”. This could have serious consequences. What do you do?

Click on our guide for the steps you should follow.

Publishers guide

Africa Check teams up with Facebook

Africa Check is a partner in Meta's third-party fact-checking programme to help stop the spread of false information on social media.

The content we rate as “false” will be downgraded on Facebook and Instagram. This means fewer people will see it.

You can also help identify false information on Facebook. This guide explains how.

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.
limit: 600 characters

Want to keep reading our fact-checks?

We will never charge you for verified, reliable information. Help us keep it that way by supporting our work.

Become a newsletter subscriber

Support independent fact-checking in Africa.